Daruruwan al′uman Spain suna zanga zanga kan kare mutuncin iyali | Labarai | DW | 30.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Daruruwan al'uman Spain suna zanga zanga kan kare mutuncin iyali

ɗaruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga kan titunan birnin Madrid na ƙasar Spain, don ƙarfafa goyan bayansu kan kare mutuncin iyali. Masu zanga-zanagar sun yi tafi, tare da nuna jin dadi, lokacin da aka nuna paparoma Benedict na 16 kan telebijin yana shugabantar addu’ar karshen shekara ta 2007, tare da yin jawabi kan muhinmancin aure da daukaka mutuncin iyali a addinnin kirista. Paparoman, ya aikawa al’uman kasar Spain gaisuwa ta musanman tare da yaba musu da nisanta kansu da sabuwar doka da ta bada damar aurantaka tsakannin jinsi daya da gwamnatin Spain ta sanyawa hannu a kwannakin baya.