Darfur: Kuri′ar raba gardama cikin rashin tabbas | Siyasa | DW | 13.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Darfur: Kuri'ar raba gardama cikin rashin tabbas

Al’ummar yankin Darfur na kasar Sudan sun kada kuri´a a fafutukar neman samun 'yancin gashin kansu daga hannun gwamnatin kasar, amma suna cin karo da turjiya daga hukumomi.

Neman 'yancin gashin kan 'yan yankin na Darfur da ek yammacin kasar Sudan yasa aka bada damar yin kuri'ar jin ra'ayin makomar yankin na Darfur. Al'ummar yankin dai sun fito da yawa don kada kuri'arsu kan ko za su hade da sauran jihohi biyar don zama yanki guda ko kuma za su ci gaba da zama a matsayinsu.

Dukkanin mazabun a yankin Dafur din dai an samu fitowar jama'a sosai kuma ba a fusakanci wata matsala ba.

Wani da ya ba da sunansa da Abdullahi na daya daga cikin wadanda suka kada kuri'arsu kuma ya bayyana yadda ya gudanar da zabensa gami da ra'ayinsa dangane da yadda yake ganin manufar zaben .

"Akwai bambamci sosai da jihohi da kuma hadesu guri guda hakan sam-sam babu tsari. Shi yasa muke tinanin a bar jihohin ya fi ma'ana da ace a hadesu a wuri guda."

Mahasin ita ma wadda ta kada kuri'a ce ta bayyana nata ra'ayin game da makomar 'yankin tana mai cewa.

"Ni na zo ranar farko don in kada kuri'ata kuma ni na fi son a bar jihohin guda biyar maimakon hadesu wuri daya. Ina da tabbacin in aka yi haka to 'ya'yanmu za su samu kyakkyawar makoma, kuma ka ga za mu iya zama cikin kwanciyar hankali da lumana da tsaro da kuma cikakken 'yanci."

Tababa game da sahihancin kuri'ar

Sudan Omar al-Bashir Präsident

Shugaban Sudan Omar al-Bashir

Shugaban kasa Omar Hassan al-Bashir wanda kotun hukunta manyan laifu ta ICC ta ke nema ruwa a jallo a bisa laifuffukan yaki wanda ya yi sanadiyyar salwantar rayukan mutane kusan dubu dari uku a kasar, ya jaddada cewar duk da halin da ake ciki a yankin, za a ci gaba da kada kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a a kan ko za su hade da sauran jihohi biyar don zama yanki guda ko kuma za su ci gaba da zama a matsayinsu na yanzu.

To sai dai a hannu daya, kungiyoyin 'yan tawaye sun kaurace wa shirin a inda suka bayyana cewar babu kamshin adalci a ciki.

Ita ma kasar Amirka a nata bangaren cewa ta yi muddin kuri'ar ta gudana a karkashin jagorancin shugaba Omar al-Bashir, akwai alamar tambaya a kan ingancin zaben.

Tun dai a shekara 2003 al'ummar yankin ke ta fafitikar samun 'yancin gashin kansu daga hannun gwamnatin Sudan a inda suke fuskantar kalubale dabam- dabam gami da tauye masu 'yancinsu na dan Adam daga hukumomin kasar.

Dafur dai Sudan yanki ne da ya yi fama da yake-yake shekara da shekaru. Yanzu dai abun saurare shi ne ko al'ummar za su amince a hada jihohin guri guda ko kuwa za'a barsu dunkule guri guda.

Sauti da bidiyo akan labarin