1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daren Lailatul Kadri

Abba BashirOctober 2, 2006

Yaushe ake sa rai da Daren Lailatul Qadri

https://p.dw.com/p/BvVD
Watan Ramadan
Watan RamadanHoto: AP

Jamaa masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fitone daga hannun Malama Binta Usman, Karamar Hukumar Auyo, Jihar Jigawa, a Tarayyar Najeriya.Malamar cewa ta yi; Shin yaushe ake sa rai da daren Lailatul-Qadr?

Amsa: Domin jin amsar wannan tabaya, Mun tuntubi Dr. Aminuddeen Abubakar, Shaihun Malami a tarayyar Najeriya. Ga kuma abinda yak e cewa game da amsar wannan tambaya.

Aminuddeen: Daren Alqadari, dare ne mai girma, dare ne mai daraja. Allah, da kansa ya bayar da tarihin wannan dare a cikin Al-Qur’ani Mai-girma; Inda yake cewa; Lailatul Qadri, dare ne da aka saukar da Al-Qur’ani a cikin sa. Har ila yau kuma , dare ne mafi alkhairi daga cikin wasu watanni Dubu. Mala’iku tare da Mala’ika Jibrilu suna sauka a cikin wannan dare da izinin Ubangijin su, saboda kowanne irin umarni. Kuma aminci ne a cikin wannan dare tun daga faduwar Rana har zuwa ketowar Alfijir.

Bashir: Malam, to a yaushe a ke sa rai da shi wannan dare na Al-qadari?

Aminuddeen: Zance mafi rinjaye kuma mafi shahara, shine cewar an fi sa ran wannan dare na lailatul-qadri a daren 27, wato ranar da aka kai azumi 26, to a wannan rana da daddare shine daren 27. Amma duk da haka ana tsammatar wannan dare, tun daga daren 21,23,25.27, wadansu ma suna hadawa da daren 29 amma wadansu suka ce a’a, daren 29 ba dare ne na lailatul-qadri ba, dare ne na gobe Sallah. Sabodahaka daren gobe Sallah, shima ya na da tasa darajar, yana da tasa falalar.

Bashir: To Malam idan Mutum ya dace da wannan dare mai yak amata ya ce?

Aminuddeen: Nana A’isha, matar Manzo Sallallahu Alaihi Wasallam,ta taba tambayarsa wannan, sai ya bata amsa da cewa; Idan kika dace da daren Lailatul-qadri, to ki ce; Allahumma innaka afuwun, tu hibbul afwa, fa’afu anni. Wato ma’ana; Allah,hakika kai ne mai afuwa, kana son afwa, kaimin afwa.

Bashir: To Malam, Shin gaskiya ne a daren lailatul-qadri ana ganin komai yana yin sujada, kamar Bishiyoyi da Gidaje, akan ce ma wai Mutum yana iya hango ka’aba daga duk inda ya ke?

Aminuddeen: A gaskiya irin wadannan bayanai basu tabbata da ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam ) ba,ko kuma magabata na kwarai. Fadin haka kokari ne kawai na wadansu Mutane ba tare da wani dalili na shari’a ba. Amma fa Allah zai iya aikata abinda ya ga dama, to amma mu tsaya ga nassi, Allah ya ce, Annabi ya ce , shi ne ya fi.