Darajawa yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin gaza | Labarai | DW | 26.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Darajawa yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin gaza

Prime ministan Izraela Ehud Olmert ya bayyana cewa, Izraela zata nunar da abunda ya kira hakuri da juriya adangane da martani kann harin rokoki da palasdinawa suka kaiwa yankunan ta saoi,da fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ayau.Rundunar Sojin kungiyar Hamas ta dauki alhakin harba rokokin daga zirin gaza zuwa cikin izraela ,adangane da abunda ta kira cigaban kasancewar dakarun Izraelan acikin gazan.Kazalika kungiyar Jihad Islami,suma sun dauki alhakin kai hari yankunan izraelan ,da sharadin cewa zata daina ne kadai,idan dakarun izraelan suka janye daga garuruwan gabar yamma da kogin jordan.Akarkashin yarjejeniyar dai ,ana bukatar kungiyoyin sakai na palasdinawan su dakatar da harba rokoki zuwa cikin Izraela,kana ita kuwa Izraela ta janye dakarunta da ga zirin gaza a madadin hakan.Prime ministan Ismail Haniya na Palasdinawa yace dukkan kungiyoyin sun cimma yarjejeniyar dakatar da harba rokokin.