Daniel Ortega na shirin lashe zaɓen shugaban ƙasa Nicaragua | Labarai | DW | 07.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Daniel Ortega na shirin lashe zaɓen shugaban ƙasa Nicaragua

Bayan bayyana kashi 61 bisa 100, na ƙuri´un da aka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasa zagaye na farko ,a Nicaraguwa, akwai alamun tsofan shugaban ƙasa, Daniele Ortega, ya dawo kan karragar mulki, bayan shekaru 16 da barin ta.

Ya zuwa yanzu,Daniele Oretega ya yi fintinkau ga sauran yan takara da su ka shiga zaben.

Idan har wannan nasara ta tabbata, manazarta al´ammuran siyasa, na ganin Amurika, zata ƙara shiga wani mugun hali, a dangantarkar ta, da ƙasashen yankin Latine Amurika.

Ortega na daya daga aminan shugaba Ugo chavez na Venezuella, sannan ba shi ga macciji da magabata Amurika alokacinda ya rike karagar mulki., daga 1979 zuwa 1990.

Masu sa iddo ga wannan zaɓe, sun tabatar da cewa ya wakana lami lahia, duk da zargin da Amurika ta yi na cewar an tabka maguɗi.