Dangantakar Zimbabwe da Cuba | Siyasa | DW | 20.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dangantakar Zimbabwe da Cuba

Ingantuwan dangantaka tsakanin Cuba da Zimbabwe

default

Shugaban Zimbabwe,Robert Mugabe

Cuba ta sanar da manufofin ta na tallafawa Zimbabwe dake fama da matsalolin rayuwa,sakamakon rigingimu na siyasa daya durkusar da tattalin arzikin wannan ƙasa.

Jakadan ƙasar Cuba a Zimbabwe Cosme Torres Espinoza ya bayyanawa manema labaru a birnin Harare cewar,ƙasar sa zata taimakawa Zimbabwe din ne sakamakon yadda ƙasashen yammaci na turai suke gasawa wannan kasa aya a hannu,dangane da yadda ta kwace gonaki a hannun turawa fararen fatan kasar domin rabawa bakake yan asali.

Ya ce Amurka ta mayar da kasarsa ta Cuba saniyar ware kamar yadda ta mayar da Zimbabwe.A yanzu haka dai an sanyawa Cuban takunkumin tatattalin arziki.

Amurka da Kungiyar tarayyar turai da sauran ƙasashen Turan sun kakabawa jamian gwamnatin kasar takunkumin tafiye tafiye,tare da dakatar da asusun fiye da manyan jamian jamiiyyar dake mulki a kasar ta Zimbabwe 100 kaddarorin su dake ketare .Wannan dai inji turawan ya zamanto wajibi dangane da yadda hukumomin Zimbabwen ke cigaba da take hakkokin biladama.


Robert Mugabe dai ya danganta wadannan takunkumin da durkushewar tattalin arzikin wannan ƙasa dake yankin kudancin Afrika.

Ƙasar ta Cuba dai na taimakawa Asibitocin Zimbabwe da Likitoci da sauran jamian kula da lafiya,musamman ma dayake jamian Asibitocin na watsi da ayyukansu,domin neman ingantuwan rayuwa a ƙasashen ketare.

Jakada Espinoza ya fadawa manema labaru cewar,Cuba ta samu gagarumar nasara a juyin juya halin ta ,saboda alummomin kasar sun fahin ci manufofin yin hakan ,kuma sun ci gajiyar 'yancin kai.

Adangane da hakane yace ƙasarsa na shirye wajen taimakawa Zimababwe ,wajen farfaɗo da tattalin arzikin ta daya durkushe,tare da taimaka mata wajen samar da walwala na siyasa da rayuwa.

A wannan makon nedai Jakadan Amurka ya sanar da cewar kasar sa ta bawa Zimbabwe tallafin dala million 220 a shekara ta 2007 data gabata.

►◄