Dangantakar Turkiyya da KTT | Siyasa | DW | 30.06.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dangantakar Turkiyya da KTT

Hukumar Zartaswa ta KTT ta ce za a fara shawarwarin karbar kasar Turkiyya a kungiyar tun daga ranar uku ga watan oktoba mai zuwa

Tutar Turkiyya

Tutar Turkiyya

Maganar fara shawarwarin karbar kasar Turkiyya da hukumar zartaswa ta Kungiyar Tarayyar Turai (KTT) ta gabatar a Brussels a jiya laraba, ita ce ta mamaye kanun labaran tashoshin telebijin na kasar tun abin da ya kama daga yammacin jiya laraba. Tashoshin telibijin na kasar ta Turkiyya guda hudu ne suka tura wakilansu domin shaidar da taron maneman labarai da hukumar zartaswa ta KTT ta tsayar, inda ta bayyana cewar za a fara shawarwarin karbar kasar tun daga uku ga watan oktoba mai zuwa kuma za a dauki lokaci mai tsawo ana gudanar da shawarwarin, inda ba a sa ran karbar Turkiyyar sai fa nan da shekara ta 2014. Wani kwararren masanin da aka nemi jin ta bakinsa a game da wannan ci gaba cewa yayi:

Kungiyar Tarayyar Turai da kasar Turkiyya sun dogara da juna ne, wannan ko shakka babu. Kuma da zarar sassan biyu sun fahimci hakan ba zasu yi wata-wata ba wajen bin wata manufa bai daya tsakaninsu. A halin da muke ciki yanzu ba lalle ba ne mu shiga rade-radi a game da ranar da Turkiya zata zama cikakkiyar wakiliya a KTT, saboda kungiyar na da jan aiki a gabanta har ya zuwa shekara ta 2013. Kafin sannan za a ba wa kungiyar wani sabon fasali kuma Turkiyya zata zama wani bangare na wannan garambawul.

Amma fa a hakika lamarin da walakin. Domin kuwa hatta su kansu Turkawan suna da cikakkiyar masaniya a game da halin da KTT take ciki dangane da makomar daftarin tsarin mulki bai daya tsakanin kasashenta, wanda ya ci tura. Bisa ga ra’ayin da yawa daga malaman zane na jaridun Turkiyya su kann kwatanta KTT tamkar mai fama da radadin rashin lafiya. Masu adawa da shigar Turkiyya karkashin tutar kungiyar na dada samun goyan baya tsakanin jama’ar kasar yanzu haka. Wasu daga cikin Turkawan ma sai doki da murna suke yi a game da cewar kungiyar ba ta cimma nasara ba wajen wanzar da kasaitaccen shirinta na daftarin tsarin mulki bai daya tsakanin ‚ya’yanta. Ba shakka gwamnatin kasar, mai fafutukar ganin lalle sai Turkiyya ta shiga ana damawa da ita a kungiyar tarayyar Turai zata shiga kaka-nika-yi idan har an samu canjin gwamnati a fadar mulki ta Berlin, saboda zata yi asarar masu ba ta goyan baya a wannan fafutuka, sannan ta fuskanci adawar masu kyamar shigowarta inuwar kungiyar a cikin gida, duk kuwa da ikirarin da P/M Erdogan yake yi na cewar kasar ba zata yarda ta mayar da hannun agogo baya ba dangane da azamar da ta shirya na ganin lalle sai ta shigo inuwar kungiyar ta tarayyar Turai.