1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar NATO da Rasha

Abdullahi Tanko BalaMarch 6, 2008

Taron Majalisar hadin gwiwa ta kungiyar NATO da Rasha domin bitar dangantakar dake tsakanin su.

https://p.dw.com/p/DJsr
Taron Ministocin harkokin wajen NATO da RashaHoto: AP

A ranar jumaár nan ce zaá gudanar da taron majalisar haɗin gwiwa ta ƙungiyar tsaro ta NATO da kuma Rasha domin bitar dangantakar dake tsakanin su bayan sauyin shugabanci da aka samu a ƙasar ta Rasha. Abdullahi Tanko Bala na ɗauke da ƙarin bayani.

A shekarar 1997 ne dai aka kafa kwamitin tuntubar junar tsakanin NATO da Rasha, sannu a hankali a shekarar 2002 suka daga likafar kwamitin ya zuwa majalisar hadin gwiwa ta bangarorin biyu. Manazarta na tababa akan ko zaben Dmitry Medvedev a matsayin sabon shugaban kasar Rasha zai sauya akalar manufofin harkokin wajen kasar duk da cewa gwamnatin da ta shude ta Vladmir Putin ce ta dora shi tare da amincewa zaá baiwa Putin din mukamin Firaminista.

A yayin wannan taro ne ake sa ran Mosco za ta fayyace matsayin dangantakar ta da kuma inda ta dosa. A can baya an sha samun takun saka tsakanin kungiyar kawancen tsaron ta NATO da kuma Rasha. Taron na da muhimmancin sosai kasancewar shine na farko da zaá gudanar tsakanin kungiyar ta NATO da sabuwar gwamnatin ta Rasha. Abin laákari dai shine cewa kasashe kimanin ashirin dake cikin kungiyar ta NATO wadanda a da suke abokan gaba da Rasha a yau sun zamo abokan juna na kurkusa.

A ranar 28 ga watan Mayu shekara ta 2002 Sakataren NATO a wancan lokaci Lord Robertson da ya bude taron majalisar hadin gwiwar ta farko a birnin Rome tsakanin NATO da Rasha, inda ya baiyana cewa babban abin alfahari ne. Yace yana da matukar wahala a iya kawar da kai ga muhimmancin wannan taro na farko na NATO da kuma Rasha, kasashe ashirin suka hallara domin hada hannu ba tare da nuna wani fifiko ba, kuma akan manufa guda domin samar da zaman lafiya a wannan duniyar ta mu. Wannan ya kawar tsawon shekaru da aka yi na fargaba da rashin yarda, kana ya kuma nuna cewa kasashe wadanda a da suke gaba da juna a yau sun zama abokan juna.

Da yake tsokaci shugaban Amirka George W Bush ya baiyana dangantaka tsakanin kasashen gabashi dana yammaci da cewa muhimmin mataki ne wajen yaki da yan taádda musamman bisa laákari da harin 11 ga watan Satumba akan kasar Amirka. Bush yace yayin da muka mika hannun kawance da sabuwar Rasha wadda ta kudiri aniyar samar da yanci dan Adam a kasar ta, da kuma tuni ta shigo cikin mu domin yaki da abokan gaban mu na bai daya, mun kuma yi hakan da zuciya daya ta wanzuwar zaman lafiya da abokantaka.

Shima tsohon shugaban gwamnatin Jamus Gehard Schroeder ya tofa albarkacin bakin sa kan muhimmancin kawancen dake tsakanin Rasha da kungiyar tsaron ta NATO. Yace bayan dabbaka yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin Rasha da NATO, dukkanin wata gaba a tsakanin su ta zamo tarihi. Rashin jituwa a Nahiyar Turai tsakanin gabashi da yammaci ya kau. kuma ga mu jamusawa abin farin ciki ne yadda shugaban Amirka George W Bush da Vladimir Putin suka gabatar da jawabai a majalisar dokokin Jamus na kawo karshen yakin cacar baka.

A bisa aláda akan gudanar da wannan taro na majalisar hadin gwiwa tsakanin Rasha da NATO sau biyu a kowace shekara inda Ministocin harkokin wajen dana tsaron kasashen suke haduwa domin tattauna batutuwan da suka shafi yadda za su karfafa dangantakar dake tsakanin su.


Kafa majalisar ta dundundun tsakanin Rasha da NATO ta dinke baraka a lokacin yakin cacar baka. Sai dai kuma hakan bai kawar da sabanin raáyi a tsakanin bangarorin biyu ba. A lokacin taron da sukan gudanar na wata wata Mosco ta koka kan cewa kawancen na aiki ne da tsoffin yarjejeniya da aka cimma a saboda haka ta gabatar da bukatar sabunta wannan yarjejeniyar su dace da zamani.

Baya ga fadada wakilcin NATO da kungiyar ta yi na shigar da wasu kasashen gabashin Turai wani batu kuma da Rasha ke takaddama akai shine burin da Amirka ta sanya a gaba na kafa cibiyar kariyar makamai masu linzami a gabashin Turan. Babu dai tabbas ko sabon shugaban kasar ta Rasha Medvedev zai aminta da wannan shawara.