Dangantakar Musulmi da Jamusawa bayan 11.9 | Siyasa | DW | 11.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dangantakar Musulmi da Jamusawa bayan 11.9

Masallatai a birnin Berlin sun mayar da hankali akan 11.9. a hudubar juma'ar da ta wuce

A cikin hudubar da ya gabatar a harshen Jamusanci, limamin babban masallacin Amir-Sultan dake yankin Schöneberg a birnin Berlin cewa yayi:

“Har abada ba zamu dadara ba muna masu Allah Waddai da duk wani mataki na tashin hankali da ta’addanci da sauran manufofi na ta’asa. Babba abin da musulunci ya sa gaba shi ne samar da adalci tsakanin jama’a. Wajibi ne kowane dan-Adam ya samu sa’ida a rayuwarsa ta yau da kullum ba tare da la’akari da tushensa ko addininsa ba. Bai kamata ayi amfani da wani buri na dabam domin fatali da wannan manufa ba. A saboda haka wajibi ne akan dukkan musulmi su zama abin koyi wajen kamanta adalci da bin gaskiya a rayuwarsu ta yau da kullum.”

Wannan a takaice shi ne hudubar da limamin masallacin Amir-Sultan ya gabatar, inda ya rika nanata cewar musulunci na adawa matuka ainun da matakai na ta’addanci, lamarin da Mustafa Kömer da Feyzula Hizilkaya suka yi na’am da shi. Mustafa Kömer ya ce:

“Ya fadi gaskiya a hudubar tasa. Ya bayyanar a fili cewar ta’addanci ba alheri ba ne, kuma mutane da dama na kuskure wajen fassara musulunci, musamman ma su ‘yan ta’adda. Kazalika ya ce babban kuskure ne a rika shafa wa dukkan musulmi wannan kashin kaza. Wajibi ne kowane musulmi ya fito fili ya kakkabe hannunwansa daga duk wani mataki na ta’addanci.”

Muhimmin abu a game da sallar juma’ar da ta gabata shi ne kasancewar a karo na farko kimanin masallatai 40 dake birnin Berlin sun gabatar da huduba iri daya. Kowane daga cikin limaman masallatan ya tsayar da shawarar tabo maganar harin ta’addancin 11 ga watan satumban shekara ta 2001 a hudubarsa. Domin kuwa harin ba kawai ya shafi Amurka ba ne, kazalika a daya bangaren ya zama tamkar mizanin auna dangantakar musulmi da Jamusawa a nan kasar in ji Riem Spielhaus daga wata kungiyar musulmi dake birnin Berlin. Dukkan bangarorin biyu sun fahimci cewar wajibi ne su rika tuntubar juna. Domin cimma wannan burin aka kirkiro kungiyar ta Berlin a wajejen karshen shekarar da ta wuce, kuma gamayyar ta zama tamkar wata uwar gaggan kungiyoyin musulmi ne dake bakin kokarinta wajen share fagen musayar ra’ayoyi akai-akai tare da mujami’u da ma’aikatar cikin gidan Berlin da ‘yan sanda da sauran mahukunta dake birnin.