Dangantakar Libiya da sauran kasashen Afurka | Siyasa | DW | 05.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dangantakar Libiya da sauran kasashen Afurka

Bayan shekaru da dama da tayi a matsayin saniyar ware a yanzu Libiya ta sake dawowa tsakanin sauran dangi domin a rika damawa da ita dangantakar kasa da kasa

Shugaba Ghddafi na Libiya

Shugaba Ghddafi na Libiya

An saurara daga bakin shugaban juyin juya halin Libiya kanar Mu’ammar Ghaddafi, wanda a baya ga shugaban mulkin kama karya na kasar Togo Eyadema, shi ne ya fi kowane shugaba dadewa kan karagar mulki a nahiyar Afurka yana mai bayani a game da irin canjin da aka samu a dangantakar kasarsa da sauran sassa na duniya, inda yake cewar:

An samu wani kyakkyawan canji mai ma’ana tare da fahimtar juna. Domin kuwa an wayi gari tsaffin abokan gabarmu suna miko mana hannun sulhu domin shiga wani sabon yayi na kawance da juna.

Shugaba Ghaddafi ya gabatar da wannan kalamin ne ga jami’in diplomasiyyar Amurka William Burns. Wannan lafazi, kazalika yana mai yin nuni ne da canjin da aka samu ga manufofin Libiya, kasar da aka yi shekara da shekaru ana mayar da ita saniyar ware a dangantakar kasa da kasa. Sau tari, masu kalubalantar manufofin Ghaddafi, su kan yi hakan ne ba tare da wata masaniya ba a game da halin da Libiya ke ciki da kuma kyamar fahimtar manufofin shugaba Ghaddafi. Babban misali a nan shi ne wani abin da ya faru a majalisar wakilan kasar libiya a tsakiyar shekarun 1970, lokacin da wakilan suka shiga yi wa kasashen ketare Tofin Allah Tsine. Shugaba Ghaddafi bai yi wata-wata ba wajen darewa kan membari ya karbe makrufo ya jefar a kasa ya kuma tattake shi sannan ya sake daukarsa a hannu yana mai cewar in har akwai wanda zai iya gyara wannan na’urar a nan zauren to kuwa ba shakka muna da dalili da kuma ikon kalubalantar ‚yan kasashen ketare da kuma fatattakarsu daga harabar kasarmu. Dukkan wakilan suka yi tsit kamar ruwa ya ci su, kuma nan take aka yi watsi da wannan shawara. Wasu daga manazarta na kasa da kasa sun kalubalanci Ghaddafi, a maimakon su yaba masa da wannan rawar da ya taka, saboda ba sa fahimtar Larabci ballantana dabi’un Larabawa. Suma kasashen Afurka sun sha lalube a cikin dufu a kokarin fahimtar ainifin alkiblar da Ghaddafi ya fuskanta a manufofinsa dangane da wannan nahiya. Da farko dai Libiya ta fi mayar da hankali ne ga kasashen Larabawa da na arewacin Afurka. An samu sauyin lamarin ne sakamakon goyan baya da Libiya ta samu daga kawayenta na Afurka a sabanin da kasar ta sha fama da shi da kasashen Amurka da Birtaniya da kuma MDD. Wannan goya-baya da ta samu shi ne ya taimaka kasar ta Libiya ta tsayar da shawarar daukar nauyin kafa kungiyar nan ta gamayyar kasashen Afurka dake yankin Sahel da kuma ba da cikakken goyan baya ga matakan kirkiro kungiyar tarayyar Afurka.