1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Jamus da Namibiya

April 13, 2004

Jamusawa na ba da la'akari ga tarihin mulkin mallakar kasarsu a kasashen ketare sakamakon bukukuwan tunawa da boren 'yan Herero a yankin Kudu-Maso-Yammacin Afurka (Namibia) shekaru 100 da suka wuce

https://p.dw.com/p/Bvkl
Bikin tunawa da boren Herero a Namibiya shekaru 100 da suka wuce
Bikin tunawa da boren Herero a Namibiya shekaru 100 da suka wuceHoto: dpa

A sakamakon bukukuwan da aka rika gabatarwa a game da zagayowar shekaru 100 da yakin neman ‚yancin kan kabilar Herero a Yankin Kudu-Maso-Yammacin Afurka dake karkashin mulkin mallakar Jamus a wancan lokaci Jamusawa suka fara ba da la’akari da tarihin mulkin mallakar kasarsu a ketare. Wata da ake kira Nora Schimming-Chase daga kasar Namibiya tayi shekaru da dama tana kai da komo tsakanin Namibiyar da Jamus. Ita dai Nora an haife ta ne a shekarar 1940, kuma kamar da yawa daga al’umar Namibiyar wani bangare na kakanninta Jamusawa ne. Tun tana ‚yar shekaru 13 da haifuwa Nora Schimming-Chase ta fara kutsa kanta a al’amuran siyasa. A wancan lokaci kasar Namibiya na karkashin rikon amanar Afurka ta Kudu (ATK). Kasar mai bin manufofin wariyar jinsi bata yi wata-wata ba wajen gabatar da wani shiri na rabe yankunan farare da kuma bakar fata a Windhoek, babban birnin Namibiya. Wannan mataki shi ne ya kai ga kafa kungiyar fafutukar neman ‚yancin kan yankin kudu-maso-yammacin Afurka ta SWANU a shekarar 1959, wadda Nora ta shiga karkashin inuwarta. Kungiyar ta SWANU tayi hadin kai da sauran kungiyoyi na kasar domin adawa da shirin canza wa bakar fata mazauni. Kimanin mutane 11 suka yi asarar rayukansu a wajejen karshen shekarar ta 1959 lokacin da ‚yan sanda suka kutsa wata unguwar bakar fata da ake kira Old location domin fatattakarsu daga wannan yanki, aka kuma tsare da dama daga cikinsu abin da ya hada har da Sam Njoma, shugaban kasar Namibiya dake ci a yanzu, sannan ragowar kuma suka tsere domin zaman hijira a kasashen Botswana da Tanzaniya. Ita ma Nora Schimming-Chase sai da ta nemi inda dare yayi mata. A lokacin da take bayani Nora tayi nuni da cewar:

Na tsere zuwa Tanzaniya kuma na gabatar da takardun neman aiki a ofisoshin jakadancin kasashe da dama. Amma ba zato ba tsammani na samu waya daga ofishin jakadancin Jamus dake sanar da ni cewar na samu skolaship domin neman karin ilimi a kasar. Bayan da na isa can domin sanya hannu akan takardar ta skolaship sai ga wata wayar kuma daga ofishin jakadancin Amurka domin sanar da ni cewar na samu skolaship a Amurka. Amma na zabi Jamus saboda kakannina sun fito ne daga kasar.

Bayan kammala karatunta Nora ta sake komawa Tanzaniya, inda tayi zaman hijira na tsawon shekaru hudu tare da mijinta dan usulin Karibiya. A shekarar 1989 Nora ta samu kafar komawa gida bayan samun ‚yancin kan kasar Namibiya sakamakon aiwatar da kudurin MDD mai lamba 435. An nada ta mataimakiyar sakataren kasa a ma’aikatar harkokin wajen Namibiya tun daga 1990, amma shekaru biyu bayan haka sai aka turota zuwa Jamus a matsayin jakadiyar Namibiya ta farko a kasar. Ta tashi haikan wajen ganin an kara kyautata dangantaka tsakanin Namibiya da Jamus, lamarin da ya sanya ta samu lambar yabo ta kasar. To sai dai kuma duk da shekaru masu yawa da tayi akan mukaminta na jakadiyar Namibiya a Jamus da kuma rawar da ta taka wajen kyautata huldodin dangantaku tsakanin sassan biyu, amma Nora Schimming-Chase ta ce, a zuciyarta, bata jin ita Bajamushiya ce. A maimakon haka ma a ganinta akwai burbushin kyamar bakar fata a kasar ta la’akari da yawan ‚yan Namiyar ruwa biyu da aka rika mayar da su gida daga nan kasar duk kuwa da cewar kakanninsu Jamusawa ne. Ta dai bayyana jin dadinta game da yadda al’amura suka canza a tsakanin matasan Namibiya, inda launin fata ko yare basu taka wata rawa illa kawai dukkansu ‚yan kasar Namibiya ne. Cimma wannan manufa, shi ne ainifin makasudin gwagwarmayar neman ‚yancin kan da aka gabatar a zamanin baya.