Dangantakar Jamus da MDD | Siyasa | DW | 21.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dangantakar Jamus da MDD

A shekara ta 1973 ne Jamus ta samu cikakken wakilci a MDD

Shelkwatar MDD a New York

Shelkwatar MDD a New York

Bayan kawo karshen yakin duniya na biyu an mayar da Jamus tamkar wata abokiyar gaba ce ga MDD, wacce aka kafa ta a shekara ta 1945 domin mayar da martani akan barnar da wannan yaki ya haddasa. Daga bisani raba Jamus da aka yi gida biyu ya hana karbar kasar a matsayin cikakkiyar wakiliya a majalisar har sai ya zuwa shekara ta 1973 lokacin da aka amince a ba wa dukkan bangarorin Jamus din guda biyu, wato Jamus ta yamma da ta gabas, cikakken wakilci. Wani abin da ya taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan ci gaba kuwa shi ne manufofin marigayi Willy Brandt na neman kusantar juna tsakanin kasashen Jamus din guda biyu. A shekara ta 1972 aka cimma yarjejeniya tsakanin Jamus ta Gabas da ta Yamma a game da cewar kowace daga cikinsu na da cikakken ikon yin gaban kanta wajen bin manufofinta na ketare. Ta haka aka kawar da babban abin dake hana ruwa gudu wajen karbarsu a MDDr. Domin kuwa kafin sannan ita Jamus ta Yamma ta dage ne akan cewar lalle ita ce kadai wata halastacciyar kasar Jamus kuma ita ce zata yi magana da yawun illahirin Jamusawa a manufofi na kasa da kasa. Hakan sai ya sanya kasashen Amurka da Faransa da Birtaniya suka bayyana adawarsu ta karbar kasashen Jamus din guda biyu a MDD a yayinda ita kuma tsofuwar Tarayyar Soviet ta ce faufau ba zata yarda da a karbi Jamus ta Yamma ita kadai ba. A jawabinsa na farko ga Babbar Mashawartar MDD tsofon ministan harkokin wajen Jamus Walter Scheel ya tabo wannan matsala inda yake cewar:

Shin kuwa an fahimci dalilin dari-dari da muke yi a game da sanya kafa a MDD? Abu ne mai radadin gaske mutum ya rungumi wata kaddara ta siyasa da zata kai ga raba wata kasa gida biyu. Muna fargabar cewa daukar irin wannan mataki zai sanya a yi zaton mun rungumi kaddara ne muka amince da rarrabuwar kasar Jamus tare da fid da kauna game da sake hadewar kasar watan wata rana. Mun damu matuka ainun a game da cewar mai yiwuwa samun wakilci a MDD zai taimaka shingen dake tsakanin Jamusawa zai kara tsawo.

Wani abin lura dai dukkan kasashen Jamus din guda biyu sun ki su kai sabaninsu gaban Babbar Mashawartar MDD. A lokacin da yake jawabi game da haka tsofon shugaban gwamnatin Jamus Willy Brandt ya fada wa Babbar Mashawartar ta MDD a watan satumban 1973 cewar:

Ba mun shigo wannan zauren ne domin mayar da MDD wani daldalin daukaka kara dangane da matsalolin Jamusawa ko kuma gabatar da wasu bukatun da ita kanta majalisar ba zata iya biya mana su ba.

Babban abin da Jamus ta fi ba wa fifiko a MDD shi ne ba da goyan baya ga manufofin girmama hakkin dan-Adam da yaki da talauci da kuma tabbatar da zaman lafiyar duniya. Ba a samu wani sauyi game da wadannan manufofi ba hatta bayan sake hadewar kasashen Jamus din guda biyu shekaru goma sha biyar da suka wuce. Kuma a sakamakon wadannan manufofi nata da kuma gudummawa mai tsoka da take bayarwa ga baitul-malin MDD hadaddiyar kasar ta Jamus ke neman ganin an ba ta dawwamammiyar kujera a kwamitin sulhun majalisar. Ga dai abin da ministan harkokin waje Joschka Fischer ke cewa:

Wajibi ne a yi gyara ga tsare-tsaren MDD abin da ya hada har da kwamitinta na sulhu. Kuma ganin cewar maganar ba wa kasashen Turai kujera ta dindindin guda daya ba ta taso ba zamu ci gaba da kokarinmu har sai kwalliya ta mayar da kudin sabulu bisa manufa.