1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Deutschland Israel Konsultationen

January 19, 2010

A karo na farko ƙasar Jamus da Isra'ila sun yi zaman haɗin gwiwa tsakanin majalisun zartarwar ƙasashen biyu. Wannan yana nufin haɗin kai ta ɓangaren siyasa da tattalin arziki da al'adu, da kuma kekkyawar danganta.

https://p.dw.com/p/Lagi
Benjamin Netanyahu da Angela MerkelHoto: AP

A cewar Firaministan ƙasar Isra'ila Benjamin Netanyahu, wannan zaman da aka yi wani abun tarihi ne, musamman ziyarar da suka kai a wurin tunawa da kisan kiyasun da aka yi wa Yahudawa kamar yadda ya bayyan da kansa.

Netenyahu yace:

Shekaru 65 bayan kisan kiyashi da aka yi wa Yahudawa, a matsayina na Firaministan wata ƙasar Yahudu mai cin gashin kanta, da ni da ministocina mu zo harnan, wannan wani abun tarihi ne matuƙa"

An daɗe ɗasawa tsakanin ƙasashen biyu, ko da a bara an yi zaman tare tsakanin mahukuntan ƙasashen biyu a birnin Ƙudus. A wannan lokacin ƙashen suka amince dasu faɗaɗa dangantakar dake tsakaninsu, ta ɓangaren hulɗar siyasa, kamar yadda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi huruci game da wannan ziyara:

Na yi imanin cewa abu mai muhimmanci ne Jamus ta tuna da tarihi, akwai nauyin da ya rataya a kan mu na tabbatar da ingantuwa da ci gaba mai ɗorewar tare da ƙasar Isra'ila. Wato a koda yaushe bawai mu tsaya a kan batun tsaro da siyasa kawai ba, harma da hulɗarmu ya kamata mu inganta ta.

Amma shi Natanyahu butun tsaro yana daga cikin abin da ya fi daga masa hankali. Musamman irin barazanar da yake ganin daga ƙasar Iran, a faɗarsa, ƙasar da yanzu take fama da tauye ´yancin ´yan ƙasar gobe za ta zarce izuwa ga wasu ƙasashen:

Batare da ɓata lokaci ba ya kamata mu azawa Iran takunkumi mai ƙarfi, idan ba mu yi haka yanzu ba, to sai yaushe? amsa itace yanzu.

Ita ma Merkel ta amince da batun azawa Iran takunkumi, domin tattaunawar da ake yi ba ta tsinana komai ba. Inda ta ƙara da cewa yanzu haka takunkumin da aka ɗorawa Iran ya yi tasiri, kuma ana son ƙari akai.

Merkel ta kuma faɗawa Natenyahu ƙararara cewa, dole Isra'ila ta daina gina matsugunan yahudawa, domin samun ci gaba da tattaunawa tsakanin Palasɗinawa da Isra'ila inda za kai ga zaman lafiya dawwammame.

Mwallafi: Nina Werkhäuser / Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou