Dangantakar Jamus da Amurka | Siyasa | DW | 30.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dangantakar Jamus da Amurka

A jiya talata sabon ministan harkokin wajen Jamus ya gana da takwararsa ta Amurka

Steinmeier da Rice

Steinmeier da Rice

Wani abin da ya dabaibaye yanayin ganawar tasu dai shi ne rahoton garkuwar da aka yi da wata Bajamushiya a kasar Iraki. Mahukuntan kasar Amurka sun yi alkawarin ba wa Jamus cikakken goyan baya wajen binciko tahakikanin masu alhakin wannan danyyen aiki. Bayan kammala ganawarsa da sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice, Steinmeier yayi nuni da cewar:

Na gabatar da roko game da ba mu damar yin amfani da bayanai da mahukuntan Amurka suka tara dangane da sace-sacen fursinoni da kuma garkuwa da su da ake yi a kasar Iraki kuma an yi mana alkawarin ba mu wannan dama.

A baya ga halin da ake ciki a kasashen Iraki da Afghanistan da kuma ci gaba da shawarwari da kasar Iran a game da shirinta na makamashin nukiliya da ake sabani kansa, jami’an siyasar biyu, Condoleeza Rice da Frank-Walter Steinmeier kazalika sun tabo daya matsalar nan dake da sarkakiyar gaske, wacce ta shafi zargin da ake wa hukumar leken asirin Amurka CIA game da game da kame fursunoni a asurce kuma ba a bisa ka’ida ba a wasu kasashen Turai, abin da ya hada har da Jamus. Dangane da haka Steinmeier yake cewar:

Na yi farin ciki matuka ainun a game da cewar mun tattauna wannan batun dalla-dalla. A gani na yin hakan abu ne da ba makawa game da shi a irin wannan ganawa, kuma abin farin ciki shi ne an fahimci irin damuwar dake tattare a zukatan jama’a a nahiyar Turai a game da wannan mummunan ci gaba, wanda wajibi ne a dauki matakan binciko ainifin gaskiyar lamarin.

Wannan dai ga alamu wani yunkuri ne ma’aikatar harkokin wajen Jamus tayi na kauce wa matsin lamba daga jama’a domin gudun sake gurbacewar yanayin dangantaku tsakanin kasar da Amurka. An dai saurara daga bakin sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice tana mai fadi kafin ganawarta da takwaranta daga Jamus Frank-Walter Steinmeier cewar a halin yanzun kome na tafiya salin alin ba tare da wata tangarda ba a dangantakar kasashen biyu. A dai mako mai zuwa ne ita kanta sakatariyar harkokin wajen Amurkan zata kawo ziyara nahiyar Turai tare da ya da zango a nan Jamus.