1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Iran da kungiyar hadin kan Turai

August 24, 2005

Kasar Iran da kungiyar hadin kan Turai sun kasa shawo kan sabanin dake tsakanin su game da tashar nuclear

https://p.dw.com/p/BvaG
Zanga-zangar neman a hana kasar Iran ta kera makaman nuclear
Zanga-zangar neman a hana kasar Iran ta kera makaman nuclearHoto: AP

Kungiyar hadin kann Turai ta soke wani taro da aka shirya gudanarwa ranar talatin da daya ga watan Agusta, tsakanin ta da kasar Iran, wanda a lokacin sa, za’a tattaunawa hanyoyin warware sabanin dake tsakanin bangarorin biyu game da tashar nuclear da kasar Iran take ginawa. Amerika a daya hannun, tayi kira ga kasashen na Turai su ci gaba da matsa lamba kann kasar ta Iran, game da shirin nata na nuclear. Duk da haka, kwararru suna baiyana shakkar ko kasashen na Turai suna da wata shaida da zata iya tabbatar da zargin da suke yiwa Iran, cewar tana da wani shiri na kera makaman nuclear a asirce.

Wakilan kasashen Turai guda ukku, wato Ingila, Faransa da Jamus, sunce zasu kauracewa taron da aka shirya a karshen wnanan wata ne, saboda Iran din ta lashi takobin kammala aikin da ta fara tun farko, game da tace sinadarin uranium da zata iya amfani dashi a tashar ta nuclear. Wannan mataki na Iran ya sabawa yarjejeniyar da aka amince da ita tsakanin kungiyar ta hadin kann Turai da kasar a watan Nuwamba na bara, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Faransa a Paris ta nunar. Nan da nan kuma Iran ta maida martani game da matakin Turai na dakatar da ganawar. Wakilin Teheran a shawarwarin, Hossein Mussavian ya shaidawa wani kamfanin yada labarai na Iran cewar Kasar sa zata ci gtaba da aikin tace sinadarin uranium a tashar nuclear ta Isfahan. Amma a lokaci guda Iran din duk da wnanan hali, zata ci gaba da tattaunawa da kasashen kungiyar hadin kann Turai.

To sai dai a Bruessels, jami’an kungiyar hadin kann Turai sun rasa yadda zasu bullowa al’amarin, ko kuma yadda za’a kawo karshen kiki-kaka da ake ciki yanzu, a tattaunawar ta nuclear tsakanin wnanan kungiya da Iran. Ranar biyar ga watan Agusta kasashehn Faransa, Ingila da Jamus, a madadin kungiyar hadin kann Turai, suka gabatarwa Iran tayin hadin kai tare da ita a fannonin siyasa da tattalin arziki, tare da baiwa kasar sinadarin da take bukata domin amfani a tashar ta nuclear, idan har tana son haka. Iran tayi watsi da wnanan tayi, inda a daura da haka, ta koma ga shirin ta na tace sinadarin uranium da kanta a tashar Isfahan. Ana dai sa ran hukumaar atom ta duniya, a Vienna zata gabatar da rahoto ranar ukku ga watan Satumba, a game da ziyarar da ta kai kasar ta Iran a watan jiya. Daga wnanan rahoto ne za’a yanke kudiri, ko ya kamata a gurfanar da Iran din gaban kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya.

Kasashen yamma, musamman Amerika, suna zargin Iran da cewar tana son fakewa da neman amfani da tashar ta nuclear domin samun makamashi, yadda zata kera bama-bamai na atom a asirce. To amma kwararru na Amerika da na sauran duniya, a halin da ake ciki, suna shakkar ko zargin da Amerika take yi yana da wata makama a zahiri. Jaridar Washington Post ta rawaito cewar guggubin tataccen sinadarin uranium da aka gano a a tashar ta Isfahan, ba a kasar Iran aka tace shi ba, amma bisa dukkan alamu, ya fito ne daga kasar Pakistan, wadda ake zargin cewar tun shekaru da dama da suka wuce, ta baiwa Iran din na’urar tace sinadarin na uranium. Gwamnatin Amerika dai tasha amfani da tataccen sinadarin na Uranium da aka samu a Iran a matsayin wata shaida dake nunar da shirin kasar na kera makaman nuclear.

Wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amerika a daura da haka, yace akwai alamu da dama dake ci gaba da haddasa damuwa. Akwai tambayoyi masu yawa tattare da na’urorin na Iran dake iya tace sinadarin uranium, musaman kuma yadda Iran din take kin hada kai da hukumar hana yaduwar makaman atom a duniya.