Dangantakar Iran da Amirka | Siyasa | DW | 13.01.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dangantakar Iran da Amirka

Amirka ta musunta zargin cewar tana da hannu a kisan masanin fasahar nuclear na Iran

default

Kofar jami'ar birnin Teheran

Wannan hadari na tashim bom da ya zama sanadiyyar mutuwar masanin fasahar nuclear Massoud Ali-Mohammadi ranar Talata yazo ne a daidai lokacin da ake fama da fadi-tashi a kasar ta Iran, abin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa da zanga-zangar yan adawa. Nan da nan kuwa bayan kisan masanin, Iran ta nuna yatsar zargi ga Amerika da Israila, wadanda tace sun hada baki domin kashe daya daga cikin masanan ta, a yunkurin dakatar da ci gaban shirin ta na nuclear. Ya zuwa yanzu dai babu wani bayani game da wata kungiya ko wadanda suke da alhakin tayar da wannan bom, ko kuma yawan wadanda suka mutu a sakamakon sa.

Kasashen yamma suna zargin cewar Iran tana bin manufofin ta na nuclear ne ba saboda kokarin samun makamashi ba, kamar yadda tace, amma burin ta shine ta tanadar wa kanta makaman nuclear. Zaunannun wakilai biyar na kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya tare da Jamus, ana sa ran ranar Asabar mai zuwa zasu sake zaman taro a New York, inda zasu yi nazarin mataki na gaba, bayan da Iran ta nuna alamun ba zata yi sassaucci kan matsayin ta game da shirin nuclear ba, duk kuwa da shawarwari tareda kasashen na yamma. Wadannan kasashe shidda sun yi gargadin cewar lokaci yana kurewa, kasar tana iya fuskantar hare-haren soja, kamar yadda yan diplomasiya a Washington suka yi bayanin halin da ake ciki. Suka ce shugaban Amerika yana kara fama da mnatsin lamba ya dauki wani mataki kan kasar ta Iran. Obama yace:

"Amerika ta baiwa Teheran damar kama hanyar shawarwari, domin tabbatar da ganin Iran tayi amfani da fasahar ta ta nuclear domin makamashi ne kawai. Washington bata da sha'awar kaiwa Iran harin soja. To sai dai hakurin mu ba abu ne da bashi da iyaka ba. Gwamnatin Iran tilas ta fito fili ta nunawa duniya shirin ta na amfani da nuclear saboda samun makamashi ne kawai."

Obama yace kasashen yamma tareda Jamus sun gabatar wa Iran din tayi mafi dacewa, wanda ya tanadi Iran din ta kai sinadarin ta na Uranium a tace shi a ketare, musmaman a Rasha da Faransa. To sai dai Iran tayi watsi da wannan tayi, wanda burin sa shine ya hana kasar kera makamai na nuclear. Sakataren tsaron Amerika, Robert Gates yace:

"Mun damu matuka gani cewar lokaci yana ci gaba da kurewa, a yunkurin warware rikicin na nuclear kasar Iran ta hanyar diplomasiya. Gwamnatin Ahmedinejad tana da shirin kera makamai na nuclear, kuma babu mai iya sanin ko ma Iran din ta fara aiwatar da wannan shiri.

Sakatariyar harkokin wajen Amerika, Hilary Clinton tace a wani mataki na kara matsa lamba kan Iran, manyan kasashen shidda zasu sake zaman taro a New York a karshen mako, domin nazarin sabbin matakan takunkumi kan Iran. To sai dai ba'a zaton China zata shigar da kanta ga duk wani mataki na kara tsananta takunkumin kan gwamnatin a Teheran.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita Mohammed Awal