1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Hukumar BND ta Jamus da Amurka

January 12, 2006

Bisa ga dukkan alamu hukumar leken asirin Jamus BND ta taimaka wa sojan Amurka a yakin Iraki

https://p.dw.com/p/Bu2V

Jami’an hukumar leken asirin ta Jamus BND a takaice sun tabbatar da rahoton ma’amallar tsakanin hukumar da hukumar sojan Amurka a asurce. Duk da gurbacewar yanayin dangantaka tsakanin fadar mulki ta Berlin da ta White House, amma an cimma daidaituwa akan ci gaba da karfafa hadin kai tsakanin kafofin leken asirin kasa na kasashen biyu, kamar yadda aka ji daga bakin wani jami’in hukumar ta BND a wani sirin rahotanni na gidan telebijin Jamus ARD.

Shuagabannin hukumar leken asirin Jamus BND sun tsayar da wannan shawarar ce bayan tuntubar fadar shugaban gwamnati Gerhard Schröder, kuma a wancan lokaci, ministan harkokin waje mai ci a yanzun Frank-Walter Steinmeier shi ne ke shugabancin fadar ta shugaban gwamnati. Daga cikin nauyin da aka dora wa jami’an hukumar leken asirin har da taimaka wa sojan Amurka wajen binciko wuraren da ya kamata a kai musu hari a kasar Iraki, kamar dai wani harin da aka kai akan wani gini a birnin Bagadaza a watan afrilun shekara ta 2003, wanda aka yi zaton cewar shugaban kasar Iraki Saddam Hussein na cikinsa. Mutane 12 suka yi asarar rayukansu sakamakon wannan hari.

Amma rahotanni masu nasaba da jaridar Süddeutsche Zeitung sun ce hukumar ta BND ta musunta wannan batu. Amma a daya bangaren ta gaskata rahoton cewar wasu jami’an leken asirinta guda biyu su kasance a Irakin a lokacin yakin. Kazalika rahoton jaridar ta Süddeutsche Zeitung ya ce hukumar ba ta ba da bayanai a game da wuraren kai hare-hare ga daya daga cikin sassan da basa ga maciji da juna a yakin na Iraki ba. A kuwa cikin shirin rahotannin na gidan telebijin Jamus na ARD wani jami’in hukumar leken asirin ya ce mahukuntan sojan Amurka sun ba shi wata lamba ta yabo dangane da muhimmiyar rawar da ya taka.

Kawo yanzun dai ba a ji wani karin bayani a game da wannan binciken da aka gano ba, walau daga bakin tsofon shugaban hukumar leken asirin August Hanning ko ministan harkokin waje Frank Walter Steinmeier, wanda fadar shugaban gwamnati ta kasance karkashin shugabancinsa a wancan lokaci. Kakakin jam’iyyar Free Democrats a manufofi na ketare Max Stadler ya fada wa jaridar Süddeutsche Zeitung cewar idan har wadannan rahotannin sun tabbata gaskiya to kuwa hakan zai zama babban abin kunya ta yadda ba makawa a kafa wani kwamitin binciken da zai bi bahasin lamarin.