Dangantakar dake akwai a tsakanin Jamus da Poland | Labarai | DW | 08.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dangantakar dake akwai a tsakanin Jamus da Poland

Shugaban kasar Poland Lech Kaczynski na gudanar da wata ziyarar kwanaki 2 a nan Jamus, dake a matsayin irin ta ta farko tun bayan darewar sa mulki watanni biyu da suka gabata.

A lokacin ziyarar Shugaba Lech an shirya cewa zaiyi ganawar ido da ido da wasu mahukuntan kasar ciki har da shugabar gwamnati Angela Merkel da kuma shugaban kasa Horst Köhler.

Tattaunawar shugabannin dai zata shafi batu ne na makamashi da kuma tsaro a tsakanin kasashen biyu.

Kasar ta Poland data shiga cikin kungiyyar gamayyar turai a shekara ta 2004, kasa ce data dade tana da kyakkyawar alaka da kasar ta Jamus.