Dangantakar Amurka da Iran | Siyasa | DW | 14.06.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dangantakar Amurka da Iran

An fara samun sararawar al'amuran dangantaka tsakanin Amurka da Iran

A halin da ake ciki yanzu a daidai lokacin da ya rage kwanaki kalilan ga zaben shugaban kasar Iran da za a gudanar a ranar 17 ga wata, an fara hangen sararawar al’amura a dangantaka tsakanin Amurka da Iran. Wannan maganar kuwa ta jibanci sabanin da ake yi ne a game da manufofin makamashin nukiliya na kasar Iran. A cikin wata hira da aka yi da shi, Ali Akbar Hashimi Rafsanjani, wanda ake kyautata zaron cewar shi ne zai lashe zaben na ranar juma’a mai zuwa, ya fito fili ya nuna cewar ainifin maganar makamashin nukiliyar ce ta iza keyarsa domin sake tsayawa takarar zaben. Ali Akbar Hashimi Rafsanjani, wanda sau biyu yana shugabancin kasar Iran tun daga 1989 zuwa 1997, zai yi amfani da fice da yayi a dangantakar diplomasiyya ta kasa da kasa domin magance wannan takaddamar da ta ki ci ta ki cinyewa. A lokaci guda gwamnatin Amurka ta sassauta manufofinta na hannunka mai sanda ga kasar Iran. Kasar ta Amurka ta janye daga adawar da ta dade tana yi a game da karbar kasar Iran a gamayyar ciniki ta kasa da kasa ta WTO. Wasu rahotannin ma nuni suka yi da cewar shugaba Bush ya amince da shawarar ba wa kasar Iran damar tace wani adadi na ma’adanin uranium iya gwargwado. Irin wannan kusantar juna zata iya sake ba wa Iran fifiko a manufofin Amurka dangane da mashigin tekun Pasha, kamar yadda lamarin ya kasance a zamanin mulkin Shah. Wani abin da aka lura da shi shi ne kasancewar kasar Iran a ‚yan shekarun baya-bayan nan ta shiga koyi da babbar abokiyar gabarta kasar Amurka, inda hatta jami’an siyasarta dake da zazzafan ra’ayin rikau, kamar Rafsanjani, wanda ya fito fili ya bayyana cewar tilas ne Iran ta saduda ta kuma hakura da gaskiyar cewar Amurka ita ce babbar daular duniya daya kwal da ta rage. Wannan hakikancewar ta zo ne sakamakon yaduwar angizon Amurka a wannan yanki, inda take da sojojinta a Afganistan da Irak da tsaffin janhuriyoyin tarayyar Soviet a tsakiyar Asiya, wadanda gaba daya suke makobtaka da Iran. Ba shakka jami’an siyasar wannan kawanya da Amurka ke dada yi wa kasarsu abu ne dake ci musu tuwo a kwarya suka kuma lura cewar abu mafi alheri shi ne kyautata makomar dangantakarsu saboda dukkansu biyu kusan jirgi daya ne ke dauke da su. Domin dukkan kasashen biyu na sha’awar ganin an samu kwanciyar hankali tare da tabbatar da mulkin demokradiyya a Irak, saboda wannan ci gaba zai ba wa ‚yan Shi’a karin angizo a wannan kasa kuma a samu kyautatuwar dangantakar kasashen biyu. Dangane da Afghanistan kuwa, Iran ta dade tana ba wa ‚yan adawa da gwamnatin Taliban goyan baya, wadanda suka samu ikon kifar da gwamnatin Taliban din tare da taimakon Amurka. Kasar Iran daidai da kasar Amurka babu daya daga cikinsu dake sha’awar kafuwar wata gwamnati mai zazzafan ra’ayi na addini a Afghanistan ko wata kasa ta yankin tsakiyar Asiya ko kuma Pakistan. A takaice dai a halin da ake ciki yanzu rikicin Palasdinu ne kawai, kasashen biyu ke sabani kansa. A yayinda shugaba Bush ya fara nuna sassauci a game da matsayinsa dangane da Palasdinawa a yanzun, ita ma Iran ta ce ba zata hana ruwa gudu ga duk wata manufar da zata samar da kusantar juna tsakanin Palasdinawa da IsraIla ba, ko da yake har yau tana kyamar manufofin Isra’ila.