1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump da Kim sun cimma matsaya

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 12, 2018

Shugaban Amirka Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un sun yi alkawarin yin aiki tare don raba yankin Koriya da makaman nukiliya.

https://p.dw.com/p/2zMwI
Bildergalerie Kim Trump
Hoto: Reuters/J. Ernst

Wannan na zuwa ne bayan da a ka kwashe tsawon sa'o'i hudu shugabannin kasashen biyu na tattaunawa a Tsibirin Sentosa na kasar Singapore, Amirka da Koriya ta Arewa da suka kwashe sama da rabin karni suna gaba da juna sun amince su hada hannu domin kawo karshen barakar da ke tsakaninsu. Shugabanin sun nuna matukar farin cikinsu da har suka kai ga wannan tattaunawa da ma sanya hannu a kan yarjejeniyar kawo karshen zaman doya da manjan da ke tsakanin kasashen biyu, inda Amirka ta bayyana cewa a shirye take ta bai wa Koriya ta Arewan dukkan tsaron da take bukata.

Singapur - Präsident Donald Trump gemeinsam Unterschriebenes Dokument nach Treffen mit Kim Jong Un
Shugaba Trump ya nunawa manema labarai takardar da suka sanyawa hannuHoto: Reuters/J. Ernst

Martanin al'ummomin kasa da kasa

Tuni al'ummomin kasa da kasa suka fara furta albarkacin bakinsu dangane da wannan ganawa mai dinbin tarihi da ta gudana tsakanin Shugaba Trump da Shugaba Kim. Da yake bayyana ra'ayinsa kan ganawar shugabannin biyu, shugaban makawabciyar kasa Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya ce lallai an cimma nasara, ya kuma sha alwashin kafa sabon tarihi tsakaninsa da makwabciyarsa Koriya ta Arewa da a baya ke zaman abokiyar takun sakar kasarsa.

Singapur Sentosa USA-Nordkorea Gipfel Anfahrt Trump
An yi zaman ne a tsibirin Sentosa na kasar Singapore Hoto: Getty Images/AFP/R. Rahman

A nata bangaren kasar China ta bakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta nuna jin dadinta dangane da matsayar da Amirka da Koriya ta Arewan suka cimma, tare da fatan dukkanin bangarorin biyu za asu yi aiki tare musamman kan batun raba yankin Koriya da makaman nukiliya. Shima ministan harkokin kasashen ketare na kasar Rasha Sergei Lavrov ya yaba da ganawar, yana mai cewa hakan wani babban ci-gaba ne. Ita ma dai kungiyar Tarayyar Turai EU, ta bakin babbar jakadar hulda da kasashen ketare ta Tarayyar Turan Federica Mogherini ta bayyana cimma matsayar tsakanin kasashen biyu da wani gagarumin ci gaba da zai taimaka wajen raba yankin Koriya da makaman nukiliya. Tuni dai Shugaba Donald Trump na Amirka ya bar kasar ta Singapor domin ya koma gida.