1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Amirka da Iran

Abdullahi Tanko BalaJuly 18, 2008

A karon farko Amirka zata tura babban jamiín ta domin tattaunawa da wakilan Iran

https://p.dw.com/p/Eeti
Shugaban ƙasar Amirka George W. BushHoto: AP Photo

A ranar Asabar mai zuwa ne zaá gudanar da tattaunawa a birnin Geneva kan batun makamashin Nukiliyar Iran, inda a karon farko Amirka zata tura babban jamiín ta na Diplomasiyya William Burns don ganawa da tawagar Iran. To ko wannan na nufin sauyin manufa Amirkan ta yi akan Iran wadda tun da farko shugaba Bush ya kira a matsayin shaiɗaniyar ƙasa ?

Bayan tsawon shekaru na tsamin dangantaka tsakanin Amirka da Iran a yanzu alámura sun fara ɗaukar sabon salo na kyautatuwar muámala a tsakanin su. Bayan yunkurin maida hulɗar jakadanci da Iran da Amirkan ke shirin yi, tana kuma fatan buɗe sufurin jiragen sama a tsakanin ƙasashen biyu. Wannan zai kasance ne idan shugaban Iran Mahmoud Ahmedinejad ya amince da hakan.


Tun a shekarar 2002 dangantakar shugaba George W. Bush da ƙasar Iran a baiyane take kamar yadda ya sha faɗa a cikin jawaban sa, yana mai cewa irin waɗannan ƙasashe da takwarorin su yan taádda sun kasance rukuni na shaiɗanun ƙasashe.


A yanzu dai a yan watanni bakwai da suka rage masa a ƙaragar mulki, Bush ya nuna sauyin matsayi a bisa manufa ga ƙasar Iran. Hasali ma dai a ranar Asabar din nan babban jakadan Amirka William Burns zai isa birnin Geneva domin tattaunawa da babban mashawarcin Iran kan shirin Nukiliya.


A baya Amirka ta sha faɗin cewa ba zata yi wata tattaunawa kai tsaye da Iran ba, matuƙar bata dakatar da shirin ta na bunƙasa makamashin Uranium ba. To amma a ta bakin kakakin fadar gwamnatin Amirka ta White House Sean McCormack yace wannan ba yana nufin sauyin manufa bane. "Yace ko dama can suna da shaáwar yin muámala da mutanen Iran akwai kuma hanyoyi da dama da suke hulɗa da su".


Abin tambaya shine shin ina barazanar kakabawa Iran takunkumi da Amirka ke yi, kuma ko gwamnatin ta Bush ta jingine kurarin afkawa Iran ɗin da ƙarfin soji idan ta ki dakatar da shirin Nukiliyar ? Loannis Saratsis manazarci kan alámuran yaau da kullum yayi bayani da cewa "Yace a yanzu dai ana iya cewa wannan batu babu shi, ada hukumar tsaro ta Pentagon tana da wannan shiri na yiwa Iran luguden bama bamai, to amma a yanzu bana tsammanin hakan zai kasance. Kuma daɗindaɗawa alúmar Amirka basa buƙatar shiga wata rigimar, muna da matsaloli da suka sha mana kai kaga dai ga yaƙin Iraqi ga na Afghanistan sai ƙara cigaba suke yi, bama buƙatar wani yaƙin na uku.

Mai yiwuwa shugaba Bush na son ganin ya kafa tarihi a waádin mulkinsa na ƙarshe musamman na ganin cewa yayi nasara a manufofi da suka shafi ƙasashen ƙetare