Dangantakar Afrika da Jamus | Siyasa | DW | 02.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dangantakar Afrika da Jamus

Mahawara a majalisar jamus

Yan majalisar dokokin Jamus

Yan majalisar dokokin Jamus

Yan majalisar dokokin Jamus sun yi kira danagane da bukatar gwamnatin kasar ta dada inganta dangantakarta da kasashen Afrika ta hanyar bada karin tallafin raya kasashen nahiyar.

Dukkannin bangarori uku na adawa dake majalisar sun bayyana rashin gamsuwarsu dangane da yadda gwamnatin kasar jamus ke tafiyar da ayyukan raya kasashen na Afrika.Yar majalisar jammiyar the greens Kerstin Müller tace,cikin harkokin gudanarwarta,gwamnatin Berlin ta mayar da harkokin da suka danganci nahiyar a karkashin tebur....

"Me zaa iya cewa adangane da wannan dangantaka,duk da alkawura da shugabar gwamnati da ministan harkokin waje sukayiwa nahiyar Afrika,alokacin rangadin aiki da suka a kasashen dake yankin MagreB"

Itama yar majalisar dokokin daga jammiyar masu sassaucin raayi Marina Schuster,cewa tayi dukkan jakadun kasar jamus din dake kasashen nahiyar Afrika basu kware ba wajen gudanar da ayyukansu,idan aka kwatantasu da sauran jakadun kasar da sauran kasashen duniya.Akan hakane ta kara dacewa gwamnatin kasar tanayiwa harkokin kasashen Afrika rikon sakainar kashi,musamman ta fannonin inganta rayuwar alummominsu da suka hadar da kewayen dan adam da kuma harkoki na makamashi

""Gwamnatin jamus tanada manufofin da zata iya cimmawa a ta fannin raya masanaantu a kasashen Afrika da dama,domin dukkanin bangarorin biyu zasu iya kasancewa masu aiki kafada da kafada da juna"

Su kuwa yan majalisar masu raayin mazan jiya ,kokawa sukayi da adangasne da yadda kasashen turai ke cigaba da adawa da yan gudun hijira da suka fito daga nahiyar Afrika,kamar yadda Hüseyin Aydin ya bayyana...

"Dole ne a samar da kafar warware wannan matsalar domin yan Afrika da dama na fama matsalar samun halartacciyar hanyar shiga Turai"

Sai dai a nata bangaren ministar kula da harkokin raya kasashe masu tasowa Heidemarie Wieczorek-Zeul,cewa tayi jamus ta mike tsaye wajen ganin cewa an mayar da hankali kann nahiyar Afrika Afrika,kamar yadda take shirin gabatarwa a taron kasashe masu cigaban masanaantu na G 8 ,da kuma a halin yanzu da take rike da zagayen shugabancin kungiyar tarayyar turai...

""Wannan shine abunda muke ciki a yanzu ,adangane da nahiyar Afrika.Kuma zan sake nanata muku cewa a yantzu haka munas kakarin kafa koktuna kare hakkin jamaa a wannan nahiya,domin kasar jamus itace wadda tafi bayar da taimako da kuma goyon bayanta wa majalisar kasashen na Afrika"

A wannan mahawara dai an tabo batun lardin Darfur dake kasar Sudan ,inda ake neman tallafin kasashen dunikya domin ceto alummomin wannan yanki.Akan hakane minisatn harkokin waje Frankwalter Steimeier ya jaddad bukatar sake bada karin tallafin kuxdi wa dakarun kungiyar Afrika dake lardin Darfur din a halin yanzu..

"Muna dada jadda kiranmu ga kasashen turai,dangane da bukatar bada tallafi na kudade wa dakarun Afrika da suke neman gazawa saboda karancin kayan aiki.zamu tattauna wannan batu a taron ministocin harkokin waje da zamu gudanar a ranar Litinin""