Dangantaka tsaskanin Jamus da Poland bayan canjin gwamnatoci | Siyasa | DW | 23.12.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dangantaka tsaskanin Jamus da Poland bayan canjin gwamnatoci

Kawo yanzu dai ana ci-gaba da fuskantar sabani jefi jefi tsakanin kasashen biyu.

Merkel da Kaczynski

Merkel da Kaczynski

Ana iya kwatanta kasashen Jamus da Poland da cewa suna kusa amma kuma a wani lokacin suna nesa da juna. Dangantaka tsakanin Jamus da Poland dai ta kasance wani kalubale dake bukatar yin sara tare da duban bakin gatari ga kowace gwamnatin tarayyar Jamus. Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana wannan dangantaka da cewa tana tattare da ´yan sabani.

A lokacin da ta kai ziyarar aiki ta farko a birnin Warsaw a farkon wannan wata, SGJ Angela Merkel ta ce duk da sabanin da akan samu, a gareta kyakyawar dangantaka da Poland muhimmin abu ne tana mai cewa.

“Na yi imani cewar sabuwar gwamnatin Poland na sha´awar tafiyar da kyawawan dangantaku da Jamus, musamman wajen tsayar da shawarari na bai daya a batutuwan da suka shafe kasashen mu.”

Ya zuwa yanzu dai ba wani matsayi na bai daya da za´a iya cewa kasashen biyu sun dauka. Shi ma a nasa bangaren sabon shugaban kasar na Poland Lech Kaczynski ya nuni da manyan matsalolin da ke tsakanin kasashen biyu da cewa.

“Matsalar farko ita ce cibiyar yaki da fatattakar jama´a da ake shirin ginawa a birnin Berlin. Matsala ta biyu ita ce diyyar da tsofaffin wadanda aka kora ke nema daga al´umar Poland. Batu na 3 wadda su ma Jamusawa sun san da shi, shine game da aikin shimfida batutun gas tsakanin Jamus da Rasha, wanda zai kasance babban hadari ga Poland.”

Yadda za´a tinkari abubuwan da suka wakana a zamanin baya na zama wani nauyi na dindindin, kamar yadda takaddamar da ake dangane da gina cibiyar yaki da fatattakar jama´ar ta nunar. Wannan cibiyar wadda Angela Merkel ke goyon bayan aikin gina ta, zata tattara bayanai dangane da fatattakar Jamusawa daga Poland a lokacin yakin duniya na biyu. Hakan kuwa wani cin fuska ne ga kasar Poland, wadda ke fargabar canza gaskiyar abin da ya faru a wancan zamani. Bugu da kari masu kishin kasa a Poland musamman ´ya´yan jam´iyar sabon shugaba Kaczynski na son raya wata tsohuwar manufar kyamar Jamus. To amma FM Marcinkiewizc ya musanta haka.

Ba sabon abu ba ne a duk lokacin da suka gana ido da ido shugabannin kasashen biyu na nuna farin ciki da alamar kyakkyawar abokantaka, amma da zarar an yi bankwana sai a fara sukar juna. Dukkan sassan biyu dai sun cewa kalamai na fatar baka kadai ba zata wadatar ba, dole ne sai sun nuna juriya da girmama matsayin ko-wace sannan za´a iya magance matsalolin dake tsakanin su.

Yanzu haka dai Angeka Merkel ta dauki matakin farko bisa wannan manufa, inda a lokacin taron kolin kungiyar EU a birnin Brussels ta tsaya kai da fata don ganin biya bukatun kudin gwamnatin birnin Warsaw.

 • Kwanan wata 23.12.2005
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu35
 • Kwanan wata 23.12.2005
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu35