1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

101110 EU USA Debatte

November 11, 2010

Muhauwara a majalisar tarayyar Turai a game da matsayin dangantaka tsakanin Amirka da EU

https://p.dw.com/p/Q6TC
Zauren majalisar dokokin TuraiHoto: picture-alliance/ dpa

A mako mai zuwa wakilan ƙungiyar tarayyar Turai da na Amirka za su gana a gefen taron ƙolin ƙungiyar ƙawance ta NATO a birnin Lisbon na ƙasar Portugal. A farkon wannan shekarar gudanar da wannan taro ya ci-tura saboda rashin halartar shugaban Amirka Barack Obama. A lokacin dai masana sun kwatanta hakan da cewa sabon shugaban na Amirka ba ya da sha'awa sosai kan nahiyar Turai da kuma mummunan matsayin danganta tsakanin ɓangarorin biyu. A kan haka da yammacin jiya aka tabƙa muhauwara a majalisar dokokin Turai kan matsayin dangantakun.

Abin da dukkannen wakilan da suka tabƙa muhauwarar ta tsawon awa guda suka jaddada shi ne dangantaka ta ƙut da ƙut dake tsakanin ƙungiyar tarayyar Turai EU da Amirka, da yadda ɓangarorin biyu suka dogara da juna, musamman a yanzu da ƙarfin duniyar baki ɗaya ke karkata zuwa nahiyar Asiya, kamar yadda kwamishinan cinikaiya na EU Karel De Gucht ya yi nuni.

"Tattalin arzikin EU da Amirka sun fi na ko-ina a duniya dogaro da juna. Mu ne kuma ƙawayen juna mafi girma a hulɗar ciniki da zuba jari. Manufofinmu na da kama da juna dangane da alhakin warware jerin matsaloli a doron ƙasa. Duk da cewa ra'ayoyinmu su kan banbanta akan wasu batutuwan kamar kare bayanai, amma tabbatar da haɗin kai a lokutan da muka samu saɓani, abu ne dake kwantar min da hankali."

NATO Treffen Karl-Theodor Guttenberg Robert Gates
Taron ministocin tsaron NATO, ƙungiyar ƙawancen tsaro mafi girma tsakanin Amirka da ƙasashen TuraiHoto: AP

De Gucht yayi kira da a haɗa ƙarfi wajen yaƙi da manufar nan ta ba da kariya ga kamfanoni wadda ya ce illa ce ga kowa da kowa. To sai dai taƙaddamar da ake dangane da kare bayanai a harkar sufurin jirgin sama ko game da aikewa da kuɗaɗe ta banki, na daga cikin matsalolin da ake fuskanta. Da yawa daga cikin wakilan majalisar ta Turai sun nuna rashin jin daɗinsu kan yadda suka ce Amirka ba ta shiga a dama da ita sosai a wasu aikace-aikace na ɓangarorin guda biyu, musamman game da muhalli da makamashi, inji wakilin jam'iyar 'yan Socialist a Austriya Hannes Swoboda.

"Ya kamata mu faɗawa Amirkawan cewa muna da wasu ƙawaye. Muna iya gwadawa da China ko Brazil domin cimma manufar da aka sa a gaba. Dole ne Amirkawan su ji a jikinsu cewa ba wai mun dogara ne kacokan akansu ba. Muna son mu ci-gaba da tafiya da su amma ba su kaɗai ne ƙawayenmu ba musamman game da sauyin yanayi."

Barack Obama nach Kongresswahlen 2010
Shugaban Amirka Barack Obama wanda ya yi rauni sakamakon kayen da jam'yiarsa ta sha a zaɓen rabin wa'adiHoto: AP

Daga cikin masu jawabi kamar ɗan siyasar The Greens Reinhard Bütikofer na ganin sauyin akalar mulki zuwa jam'iyar Republicans a majalisar dokokin Amirka wata sabuwar dama ce ta samu ga EU game da maufofin ƙetare.

"A dangane da raunin da shugaban ya yi da kuma manufar yin gaban kai dake ƙara samun gindin zama a Amirka, na yi imani yana da muhimmanci idan nahiyar Turai ta ɗauki matakan kanta kan batutuwa na ƙasa da ƙasa. Alal misali kamar a yankin Gabas Ta Tsakiya game da batun Falasɗinawa, ko Syria ko Libanon. Ina ganin ya kamata mu nunawa Amirkawa a fili cewa a shirye muke mu ɗauki wannan nauyi."

A muhauwarar dai an nuna damuwa cewa a lokaci mawuyaci Amirka ka iya dogaro da kanta, amma za ta kwana da sanin cewa su ma ƙasashen Turai sun kawo ƙarfi kuma ba za ta iya ci-gaba da ɗaukarsu a matsayin ƙananan ƙawayenta ba.

Mawallafa: Christoph Hasselbach/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar