Danbinda dadi yayi barna a Amurka | Labarai | DW | 17.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Danbinda dadi yayi barna a Amurka

Yan sandan Amurka, sunce sun gano asulin dan bindigan nan da ya kashe mutane 32 kafin ya kashe kansa a mummunan hari da aka yi a wata jami’ar fasaha dake Virginia. Supritendant Steven Flaherty dake magana da yawun hukumar ‚yan sandan Virginia, ya shaidawa manema labarai a birnin Blacksburg cewar an gano cewar dan bindigan wani jami’i ne dan kasar Korea ta Kudu mai suna Cho Seung-Hui mai shekaru 23 da haifuwa. A wata sabuwa kuma, wadanda suka tsira da rayukan su da ‚yan uwan mamaci a harin, sun cigaba da neman bayani akan dalilin da hukumomin jami’in basu yanke shawarar rufe harabar jami’an bayan harbin farko. Har yanzu dai ba’a gano dalilin da yasa Chui ya dauki wannan mummunan mataki ba.