1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan Nijar ya kashe tsohuwar matarsa a Jamus

Ramatu Garba Baba
April 13, 2018

‘Yan sanda a Jamus suna tsare da wani mutum dan asalin kasar Nijar bayan da ya kashe 'yarsa da kuma tsohuwar matarsa ta hanyar daba musu wuka.

https://p.dw.com/p/2w0Yv
Deutschland Hamburg Messerattacke in Supermarkt
Hoto: picture-alliance/AA/N. Bayram

Rahotanni sun nunar da cewa nan take yarinyar mai shekara daya ta rasa ranta a yayin da matar da ta kasance Bajamushiya, mai shekaru talatin da hudu ta mutu a gadon asibiti a sanadiyar raunin da ta samu. Lamarin wanda ya yi matukar firgita jama'a, ya afku ne a Alhamis din da ta gabata, a wata tashar jirgin karkashin kasa da ke Hamburg birni na biyu mafi girma a Jamus.

A wata sanarwa ta bakin kakakin ‘yan sanda yankin Timo Zill ta nunar da cewa, mutumin mai shekaru talatin da uku ya arce da gudu bayan aikata kisan amman kuma daga bisani sai ya kira wayar ‘yansanda don neman mika kansa. Yanzu haka ya na tsare a ofishin 'yan sanda, inda aka kuma soma bincike a kansa. Babu karin bayani daga mahukuntan Jamus kan dalilan da suka harzuka mutumin har ya kaiga daukar matakin hallaka matar da kuma diyar da suka haifa tare.