Dan kwallo mafi kudi a Duniya | Amsoshin takardunku | DW | 02.11.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Dan kwallo mafi kudi a Duniya

Waye Dan kwallo mafi kudi a Duniya

zinedine zidane

zinedine zidane

Masu sauraron mu barkan mu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardun ku,shirin dake amsa tambayoyin masu sauraro.

Tambaya-fatawar mu ta wannan makon ta fito ne daga hanun mai sauraron mu a yau da kulum Rayyanu Hamman Walkaitu Primary Health Care Department karamar hukumar Bali dake cikin jihar Taraba a tarayar Nigeria,mai sauraron namu yace zuwa filin amsoshin takardun ku na sashen hausan Dw,bayan gaisuwa da fatan kuna lafiya,don Allah ina so a gaya mini dan kwalon kafan da ya fi kudi a duniya,dan wace kasa ne,kuma a wane kulob yake a halin yanzu.

Sai kuma fatawa ta biyu inda yace yana so a gaya masa wace kasa ta fi yawan kwararun yan wasan kwalon kafa a duniya,kuma wani filin wasa ne ya fi kowane girma a duniya,a wace kasa ne wanan filin wasa yake.

Amsa :Idan ana magana game da dan wasan da ya fi kowane kudi a duniya sai mu ce Zinedine Zidane,domin kuwa shine dan wasan da aka saya a kann tsabar kudi dola miliyan 90 cikin shekara ta 2001,wato kimanin Nairan miliyan 12,600 ke nan saboda irin kwallayen da ya jefa a raga lokacin da aka gudanar da wasanin ajin kwararu na nahiyar turai a shekara ta 2002,kuma a halin yanzu yana bugawa kulob din kwalon kafa na Real Madrid na kasar Spain wasa.

Zinedine Zidane mai shekaru 34 da haihuwa ya fito ne daga kasar faransa.

Dan wasa na biyu da ya fi tsada a duniya shine David Beckham,wanda aka ce yana samun fam 120,000 a duk mako.

Kasar kuma data fi yawan kararun yan wasan kwalon kafa a duniya ita ce,kasar Barazil, kuma a halin yanzu ita ce ke rike da kofin duniya.

Indan kuma ana magana game da filin wasan da ya fi kowanne girma a duniya sai mu ce baban filin wasa na kasar Spain dake birnin Bacelona,wanda aka baiyana da cewar yana iya daukar yan kallo 120,000 a lokaci guda,sai kuma filin wasa na biyu mafi girma a duniya dake kasar malaysia,wanda aka ce an fara ginisa tun shekara ta 1994,sai kuma shekara ta 2003 aka kamala gininsa domin karbar bakuncin wassanin Commonwealt.

Muna fata mai sauraron namu ya gamsu da wanan amsa.

 • Kwanan wata 02.11.2005
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvVk
 • Kwanan wata 02.11.2005
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvVk