Dan kunar bakin wake ya tashi bam a Bagadaza | Labarai | DW | 22.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dan kunar bakin wake ya tashi bam a Bagadaza

Da wannan Jumma'a ce yayin da mutane ke cikin masallaci, wani dan kunar bakin wake ya tashi bam da ke jikinsa a wata unguwa ta birnin Bagadaza na Iraki.

Wani dan kunar bakin wake ya tashi bam din da ke jikinsa a cikin wani masallacin 'yan Shi'a a birnin Bagadaza na kasar Iraki a wannan Jumma'a, inda ya hallaka mutane a kalla guda tara, tare da jikkata wasu mutanen 25 a cewar wasu majiyoyi na jami'an tsaro da kuma asibitoci.

A wani bangaran kuma jami'an tsaro sun harbe wani dan kunar bakin waken na biyu tun kafin ya kai ga tashin bam din da ke jikinsa, wanda shi kuma ya yi kokarin afka wa masallacin Radouaniya da ke birnin na Bagadaza.

Sannan kuma a wannan rana, wani bam din ta fashe a unguwar Abou Graïb, da ke kauyen birnin na Bagadaza bangaran Yamma, inda nan ma mutane biyu suka rasu yayin da wasu guda tara suka samu raunuka. Sai dai kawo yanzu babu wani wanda ya dauki alhakin kai wannan hari, amma dai tuni ake kallo lamarin da wani aiki irin na 'yan ta'adda na kungiyar IS.