Dan kunar bakin wake ya halaka mutune da dama a Iraki | Labarai | DW | 07.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dan kunar bakin wake ya halaka mutune da dama a Iraki

Wani dan harin kunar bakin wake ya halaka mutane 8 sannan ya jiwa da dama rauni a arewacin Iraqi. Kamar yadda ´yan sanda suka nunar dan kunar bakin waken ya yi lodin bama-bamai a cikin wata babbar mota da ya tuka ta zuwa wani wurin bainciken ababan hawa dake tal Afar inda ya ta da su. A wani labarin kuma rundunar sojin Amirka a Bagadaza ta ba da alkalumman abubuwan da suka faru a Iraqi a cikin shekaru biyun da suka wuce. Rahoton ta yayi nuni da cewa an kashe ´yan sandan Iraqi dubu 4 sannan wasu dubu 8 suka jikata a tsawon wannan lokaci. Rundunar ta ce duk da wannan mawuyacin hali a kullum ana samun masu sha´awar shiga rundunar ´yan sandan ta Iraqi. A kuma can Amirka wata kotun soji ta yankewa sojin kasar hukuncin daurin shekara daya a kurkuku bayan an same shi da hannun a kisan da aka yiwa wani farar hular a Iraqi a farkon wannan shekara.