1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan jarida ya bankado cin hanci a kotunan Ghana

Jamila Ibrahim Maizango/PAWSeptember 10, 2015

Yayin da kasashen Afirka ke famar yaki da cin hanci da rashawa, wani dan jarida a Ghana ya bankado sabbin bayanan cin hanci da rashawa, ya kuma bayyana hujjojin da ya dauko cikin sirri.

https://p.dw.com/p/1GUj7
Ghana Anas Aremeyaw Anas Undercover-Journalist
Hoto: DW/H. Fischer

Bayyanan wannan lamari dai ya janyo zaman dar-dar a babban mashara'antar kasar, kasancewar a halin yanzu babu masaniya a kan ko za'a yanke hukunci kan alkalan 180 da aka ambato sunayensu, wadanda tuni aka sallami 22 kuma ma za'a kara da wasu 12 a nan gaba. Tuni dai wasu lauyoyi suka yi allah wadai da al'amarin tare da kashedin cewar kada a yi gaugawar murna a kan bankado wadannan bayanan. Lauya Nasigri yayi mana Karin haske.

"Kwarai da gaske, wannan badakala za ta iya yin mummunar ta'adi ga ingancin hukumomin shara'ar kasar, domin fatar duk wanda ya tafi kotu samun Adalci, sai kuma ac e wasu suna bayarda kuadade ana sake masu laifin, ai ko da dan fashi da makami ne gobe ma zai maimaita har ma ya aikata kisa."

Sashen Shari'a zai gudanar da bincike

Sai dai daga safiyar ranar alhamis tara (9) ga watan Satumba ne cibiyar shara'ar kasar ta kafa wani kwamitin domin gudanar da tsaftataccen binciken lamarin domin auna yiyuwar samun hurumin tsaida wani hukunci akan alkalan da ake tuhuma.

Dadin dadewa dai cibiyoyin dake fafutikar tsaida adalci daga gwamnati, Ghana Integrity Initiative (GII) a takaice, dama cibiyar horarda ilimin tattalin arziki Instiute of Economic Affairs (IEA), tare da hukumar bincika basukan shara'a na kasa, suna alakanta cibiyar shara'ar kasar da cin rashawa ta hanyar umartan gwamnati biyan wasu basuka a gareta. Ita dai Miss Linda Ofori Kwarfo, ita ce babbar sakatariyar hadadiyar kungiyar yaki da cin hanci da rashawa a Ghana, wadda ta amince ta yi bayani amma kuma daga bisani da na kirata ban same ta ba. Su kuwa al'umma dai sun nuna mabanbantan ra'ayoyi ne.

Ghana Chief Justice Georgina Wood
Babban Mai shari'ar Ghana Georgina WoodHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Wannan dai wata badakala ce da za ta yi wuyar gogewa a tarihance sakamakon samun sunayen manyan alkalan da ke zama a kan manyan shari'un kasar, kuma a halin yanzu jama'a da dama ne suka nuna bukatar a tsare alkalan da aka ambato domin kiyaye su da aikata kisan kai, saboda halin firgicewa da yawancinsu suka shiga. Ana dai sa ran jami'in binciken sirrin Anas Armeyau Anas zai, sako cikakkun bayanan daya gano nan da wasu makwanni kadan.