Dan asalin India ya zama Gwamna a amurka | Labarai | DW | 21.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dan asalin India ya zama Gwamna a amurka

A karon farko a Amurka, Ba’indiye Dan majalisar Republican Bobby Jindal ,ya lashe zaben gwamna a jihar Louisiana.Hakan ne ya sa shi zama mutumin farko wanda ba farar fata ,daya samu wannan mukami tun daga shekarun 1870s.Jindal ,dake zama dan wasu indiyawa da sukayi gudun hijira zuwa Amurkan,wanda kuma yayi karatunsa a jamiar Oxford,ya lashe zaben da sama da kashi 50 daga cikin 100,daura da sauran yan takara 11.Bayan gabatar da kashi 87 daga cikin 100 na sakamakon zaben na jiya,Jindal yanada kashi 53 daga ciki,ayayinda mai binsa daga jammiiyyar Democrat Foster Campbell keda kashi 18 kacal.Hakan ya nunar dacewa bazaa gudanar da zagaye na biyun zaben a ranar 17 ga watan Nuwamba ,kamar yadda aka tsayar ba.Jihar ta Louisiana dai,itace ta fuskanci mahaukaciyyar guguwar Katarina da Rita a 2005.