1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkoki sun tsaya cak a birnin Kinshasa na Kwango

Mohammad Nasiru Awal
April 10, 2017

A birnin Goma na gabashin kasar an yi arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga da suka kafa shigaye suna kuma kone-konen tayoyi.

https://p.dw.com/p/2b0uZ
Kongo Polizei
Hoto: Getty Images/AFP/P. Mulongo

A wannan Litinin harkoki sun tsaya cak a Kinshasa babban birnin kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango yayin da mutane suka zauna a gida saboda fargabar barkewar tashin hankali bayan da gwamnati ta haramta gudanar da wata zanga-zangar da aka shirya yi ta adawa da Shugaba Joseph Kabila. An rufe shaguna sannan tituna sun kasance wayam a birnin mai yawan mutane miliyan10, yayin da aka girke dakarun tsaro a wurare masu muhimmanci.

Wani mazaunin birnin da ke sayar da kaya kan titi mai suna Brel Kabeya ya fada wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa ya yanke shawarar ya yi zamanshi a gida saboda yawan 'yan sanda da aka girke a ko-ina.

 

Sai dai ba a ga wata alamar zanga-zanga a Kinshasa da Lubumbashi da ke zama birni na biyu mafi girma a kasar ba. Sai dai a birnin Goma na gabashin kasar an yi arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga da suka kafa shingaye suna kuma kone-konen tayoyi.