Dambarwar siyasa a Turkiya | Labarai | DW | 29.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dambarwar siyasa a Turkiya

A kasar Turkiya dubban masu zanga zanga sun gangami a birnin Istanbul domin baiyana adawa da hade addini da harkokin gwamnati. Tsarin shigar da addini cikin harkokin gwamnatin ya zo ne bayan da yan majalisar dokoki suka kada kuriá a zagayen farko domin zaben sabon shugaban kasa. Ministan harkokin waje Abdullahi Gul wanda ke zama dan takara daya tilo a zaben yace ya nan a kann bakan sa na tsayawa takarar duk da adawar da masu zanga zangar ke nunawa. Hukumomin sojin Turkiya sun ce a shirye suke su dauki matakan da suka dace domin kare tafarkin siyasar kasar wanda ya tsame addini daga harkokin gwamnati. Wani mai magana da yawun majalisar gudanarwar kasar ya watsi da raáyin rundunar sojin cewa jamiýar ta AK wadda ke da nasaba da addini na barazana ga tafarkin Turkiya na tsame addini daga harkokin gwamnati. Gwamnatin jamus mai shugaban tarayyar turai ta yi kira ga rundunar sojin Turkiyan ta guji tsoma baki a harkokin dimokradiyar kasar.