1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

290908 Österreich Lage

Meyer-Feist, Andreas / Wien (BR)September 30, 2008

An shiga halin rashin sanin tabbas a Austria bayan zaɓen ´yan majalisar dokokin ƙasar.

https://p.dw.com/p/FRcK
Jörg Haider shugaban BZÖHoto: AP

A ranar Lahadi, masu kaɗa ƙuri'u a Austria suka zaɓi sabuwar majalisar dokoki. Bayan wannan zaɓe, yanzu al'ummar ƙasar suna fama da faɗi-tashi a game a yadda al'amuran siyasar za su gudana a ƙasar, yayin da ake sa ran za'a sha wahala kafin a kafa sabuwar gwamnati. Dalilin haka shi ne nasarorin da jam'iyu masu ra'ayin ƙyamar baƙi suka samu a wannan zaɓe.

Waɗannan jam'iyu masu ra'ayin riƙau na ƙyamar baƙi, suna ganin sune suka fi samun nasara a zaɓen na Austria, musamman magoya bayan Jörg Haider daga yankin Kärnten, dake ganin yanzu lokaci yayi da za su shiga a dama da su a harkokin siyasar ƙasar. Haidar, wanda a da can jam'iyarsa ba ta taka kara ta karya ba, yanzu yana ganin lokaci yayi da za'a yi dashi a harkokin mulkin Austria, har ma ya ce zai iya hangen kansa ɗauke da muƙamin minista a duk gwamnatin da za'a kafa nan gaba a ƙasar.

Babu shakka akwai damar hakan, inji shi. To amma abu mafi muhimmanci shine a tabbatar da daidaituwa da kare al'ummar kasa, waɗanda fannoni ne da aka yi watsi dasu matuƙa, ko kuma in karɓi ma'aikatar tattalin arziki ko ɓangaren bayar da ilimi.

Haidar ya samarwa kansa nasara a zaɓen na ranar Lahadi ne tare da jawabai masu sauƙi da suka ja hankalin jama'a: wato tabbatar da ƙarin tsaro da kiyaye doka a cikin ƙasa. Ga magoya bayan sa, Jörg Haidar shi kaɗai ne zai iya warware matsalolin da Austria take fama da su.

Jam'iyar masu ra'ayin ƙyamar baƙi ta Haidar ba ita kaɗai ce take son shiga aiyukan mulki a ƙasar ta Ausatria ba. Jam'iyar da tafi shi son mulki ma ita ce ta ´yanto Austaria, wato FPÖ, mai matsanancin ƙyamar baƙi, ƙarƙashin jagorancin Christian Strache. Haidar da shi dai da can manyan abokai ne, har zuwa lokacin da Haidar ya kafa jam'iyar kansa ta BZÖ, inda a yanzu suka zama abokan adawar juna. Shima Strache burin sa guda ɗaya ne: ya shigar da hannun sa a aiyukan mulkin ƙasar ta Austria.

Ya ce bai kamata Austria ta kasance ƙasar da mulkinta ya gagara ba, bai kuma kamata a bi ta kan jama'a ayi amfani da rashin daidaituwa domin kafa gwamnati ta marasa rinjaye ba. Wannan abu ne da ba zamu yarda da shi ba.

Hatta a ɓangaren waɗannan jam'iyu masu ra'ayin riƙau ma, an fara tunanin yiwuwar kafa gwamnatin haɗin gwiwa tsakanin su, saboda idan har suka haɗa ƙarfin su wuri guda, yawan kujerun su a majalisar dokokin zai kai yawan da ´yan jam'iyun Democrats suke da su. Waɗannan jam'iyu biyu suna iya haɗa gwiwa da jam'iyar ta Social Democrats, ko da shi ke ba tare da goyon bayan shugabanta, Werner Feymann ba, wanda burin sa shi ne ya zama shugaban gwamnati.

A halin da ake ciki kuma, bayan kayen da ta sha a zaɓen na Austaria, jam'iyar masu ra'ayin ´yan mazan jiya, wato ÖVP ta sami canji a shugabancinta. Mataimakin shugaban gwamnati, Wilhelm Molterer yayi murabus, yayin da ministan kare muhalli da aiyukan noma, Josef Pröll ya maye gurbinsa. Hakan dai ana ganin wata alama ce ta bada damar kafa sabuwar gwmanati ta haɗin gwiwar manyan jam'iyun ƙasar, wato SPÖ da ÖVP. Waɗannan jam'iyu biyu ma sun taɓa kafa gwamnati tsakanin su, amma ta rushe bayan watanni goma sha takwas.