Dambaruwar siyasa a yankunan Falasdinawa | Labarai | DW | 28.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dambaruwar siyasa a yankunan Falasdinawa

An shiga wani mummunan yanayin siyasa a yankunan Falasdinawa bayan nasarar da kungiyar Hamas ta samu a zaben ´yan majalisar dokokin Falasdinu. A gun jerin zanga-zanga da aka gudanar a birane da dama, dubbban magoya bayan kungiyar Fatah wasunsu dauke da makamai sun yi kira ga shugabannin ta da su yi murabus sannan sun yi barazanar halaka duk wani dan siyasa na wannan kungiya da ya shiga cikin wata gwamnatin hadin guiwa da kungiyar Hamas. Daga cikin wadanda suka yi zanga-zangar har da jami´an tsaron Falasdinu. A birane Gaza da kuma Ramallah dake Gabar Yamma da Kogin Jordan wasu ´yan bindiga sun afkawa gine-ginen majalisun dokoki. A kuma halin da ake ciki Baradan kungiyar Al-Aqsa mai alaka da kungiyar Fatah sun ba da sanarwar janyewa daga yarjejeniyar dakatar da yaki da Isra´la.