1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambaruwar siyasa a Liberia bayan zaben shugaban kasa

November 12, 2005
https://p.dw.com/p/BvLW

Bayan ya albarkaci zaben shugaban kasa da aka yi a Liberia a cikin wannan mako da cewa an yi adalci, kwamitin sulhu na MDD yayi kira ga al´umar kasar da su warware duk wata rigima da taso dangane da wannan zabe. Kwamitin sulhun ya ce samun nasarar gudanar da zaben cikin lumana da kwanciyar hankali wani muhimmin mataki wajen wanzuwar zaman lafiya a Liberia wadda ta yi fama da yake-yaken basasa. Yanzu haka dai bayan an kusan kammala kidayar kuri´u, yanzu haka dai Ellen Johnson Sirleaf, tsohuwar masaniyar tattalin arziki ta Bankin Duniya wadda kuma ta yi takara da tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa Goerge Weah, na kan gaba da yawan kuri´u, kuma bisa ga dukkan alamu zata zama mace ta farko da aka taba zaba a mukamin shugabar wata kasa a Afirka. A jiya magoya bayan George Weah sun gudanar da wata zanga-zanga a birnin Monrovia don nuna adawa da sakamakon zaben, inda suka ce an tabka magudi.