1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambaruwar siyasa a Kenya game da sabbin ministoci

December 9, 2005
https://p.dw.com/p/BvHK

Sabuwar gwamnatin kasar Kenya ta fada cikin wani sabon rikici bayan da wasu daga cikin mutanen da shugaba Mwai Kibaki ya nada a cikin sabuwar gwamnatin su ka ki karbar mukamansu. Manyan ´yan siyasa biyu sun yi fatali da mukaman da aka ba su a cikin majalisar ministoci suna masu cewa shugaba Kibaki ya ki koyan darasi daga kayen da ya sha a kuri´ar raba gardama da aka gudanar baya bayan nan. Wasu ´yan siyasa 17 da aka yi musu tayin basu mukaman mataimakan ministoci su ma sun ki karbar wannan tayi. A ranar 23 ga watan nuwamba shugaba Kibaki ya sallami dukkan membobin majalisar ministocinsa bayan da aka ki amincewa da sabon daftarin tsarin mulkin kasar da shugaba ke goyawa baya. ´Yar kasar da ta samu kyautar Nobel ta zaman lafiya Wangari Maathai ta yi kira ga Kibaki da ya jinkirta rantsad da sabuwar gwamnatin da aka shirya yi yau juma´a, don samun sukunin warware bambamce bambamce dake tsakanin sabbin membobin majalisar ministocin.