1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambaruwar siyasa a kasar Nepal

January 22, 2006
https://p.dw.com/p/BvB9

Akalla ´yan tawayen kungiyar Mawo-ist su 17 da kuma sojojin gwamnati 6 aka kashe a wani kazamin fada da aka gwabza a kudu maso yammacin kasar Nepal. Wata sanarwar da rundunar sojin kasar ta bayar ta ce a jiya da daddare ´yan tawayen suka farma wani ayarin motocin sojojin dake sintiri a wannan yanki. A kuma halin da ake ciki wani kawancen jam´iyun siyasa su 7 a kasar ta Nepal ya lashi takobin ci-gaba da gudanar da zanga-zangar lumana don nuna adawa da ikon Sarki Gyanendra, duk da kame daruruwan masu zanga-zangar da jami´an tsaron kasar suka yi. Kawancen jam´iyun ya shirya wani yajin aiki na gama gari a ranar alhamis mai zuwa.