1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambaruwar siyasa a kasar Bangladesh

October 28, 2006
https://p.dw.com/p/Bue9
An kashe mutane 4 sannan wasu daruruwa sun samu rauni galibi daga harsasai a tashe tashen hankula da ake yi a Bangladesh tsakanin magoya bayan ´yan adawa da na gwamnati mai barin gado da kuma ´yan sanda. Sabbin tashe tashen hankula sun zo ne kwana guda bayan mutum hudu sun rasu sannan sama da 100 sun jikata a hargitsin da aka fuskanta a fadin kasar baki daya tsakanin magoya bayan jam´iyar BNP dake mulki da kuma na jam´iyun adawa. Yanzu haka dai an girke ´yan sanda kimanin dubu 15 a manyan titunan babban birnin kasar Dhaka yayin da ake samun hauhawar tsamari bayan da wa´adin shekaru 5 na mulkin wannan gwamnati ya kare. A halin da ake ciki an soke yin bukin rantsad da wata gwamnatin wucin gadi, wadda zata shirya sabon zabe a cikin watan janeru. ´Yan adawa sun sha alwashin ci-gaba da zanga-zanga, idan gwamnati ta nada tsohon alkalin kotun kolin kasar K.M. Hasan a mukamin jagoran gwamnatin wucin gadin.