1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dambaruwar siyasa a Isra´ila

Sabon shugaban jam´iyar Labour a Isra´ila Amir Perez na kara matsa lamba a dangane da gudanar da sabon zabe na gaba da wa´adi. An jiyo Perez na cewa zai marawa daya daga cikin kananan jam´iyun adawa baya a kuri´ar rashin amincewa da gwamnati da ake shirin gudanarwa, idan har ba´a yi wata ganawa tsakanin shi da FM Ariel Sharon kafin ranar alhamis mai zuwa ba. Sharon ya dage wani taro da aka shirya yi a yau lahadi tsakanin shi da sabon shugaban na jam´iyar Labour. Perez ya sha nanata cewa zai janye daga kawancen da suke yi da jam´iyar Likud ta FM Sharon kana kuma zai bukaci da a shirya sabon zabe.