Dambaruwar siyasa a Iraki | Labarai | DW | 17.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dambaruwar siyasa a Iraki

Har yanzu ba wani ci-gaba a kokarin kafa wata gwamnati a Iraqi. A dangane da takaddamar da ake yi akan mutanen da za´a bawa manyan mukamai a cikin sabuwar gwamnati, an jingine zaman majalisar dokoki da aka shirya yi a yau litinin. Wannan zaman dai da shi ne zai zama na biyu tun bayan zaben da aka yi cikin watan desamban bara. Ana kai ruwa rana ne musamman game da kara wa´adin shugabancin FM Ibrahim al-Jaafari. ´Yan Sunni da Kurdawa na zargin FM wanda dan shi´a ne da rashin daukar tsauraran matakai akan masu ta da zaune tsaye. A ci-gaba da tashe tashen hankula da hare haren a fadin kasar ta Iraqi kuwa a jiya lahadi sama da mutane 30 suka bakwanci lahira.