1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damascus zata taimakawa Libanon da Falasdinawa

July 15, 2006
https://p.dw.com/p/BuqU

A wani labarin kuma Syria ta tabbatarwa Libanon da kuma Falasdinawa ba su goyon baya a gwagwarmayar da suke yi da Isra´ila. Bayan wani taro da ta yi a birnin Damaskus, jam´iyar Baath dake jan ragamar mulki a Syria ta ce Isra´ila na tafiyar da wani ta´addanci ne na kasa tare da taimakon Amirka. A wani taro na gaggawa da kwamitin sulhu ya yi jiya akan halin da ake ciki a yankin GTT, Libanon ta zargi Isra´ila da kaddamar da wani yaki na babu gaira babu dalili akanta, sannan ta yi kira da a kawo karshen matakan sojin. Yanzu haka dai ana yunkuri na diplomasiya da nufin kawo karshen wannan rikici. A yau babban jami´in diplomasiyar KTT Javier Solana zai yi tattakin zuwa GTT a wani yunkuri na yin sulhu. Sannan ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen Larabawa zasu shawarta a birnin Alkahira.