Dalilan da suke janyo karya darajar kudin kasa
September 16, 2015Talla
Abin da ya sa kasa take rage karfin kudi shi ne domin samun karin kudaden kasashen ketere wajen fitar da kayayyakin da aka sarrafa a kasar, kuma haka na daga cikin dalilan da China ta rage karfin kudin kasar cikin kwanakin baya.
Amma kasashe masu tasowa suka fuskantar matsala kan rage karfin kudi kamar kasashen Afirka, saboda ba sa fitar da kayayyakin da aka sarrafa, sai dai suna samar da kayayyakin da ake sarrafawa ga kasashe masu karfin tattalin arziki.