1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dalibi ya kirkiro na'urar awon zuciya a Kamarun

Sadaqi, Dunja/ Ibrahim/ SBJune 15, 2016

A wani mataki na kawo ma al'ummar kasar sa sauki, wani dalibi ya kirkiro wata na'urar awon zuciya wadda ya yi wa suna Cardiopad a kasar Kamarun.

https://p.dw.com/p/1J6v2
Kamerun Afrika Krankenhaus Frauen mit Kindern
Mata da kananan yara a wani asibitin kasar KamarunHoto: DW/E.Kindzeka

Tun dai da sanyin safiya ne cibiyar kula da harkokin lafiya ta Jami'ar Yaounde da ke kasar ta Kamarun ta cika makil da dalibai maza da mata da nufin a yi masu awon zuciya da wannan Na'ura da dalibin ya kirkiro. Abdouramane Gandai wani dalibi ne ya ce ya ga labarin wannan na'ura a kafar talbijin:

"Hakikia abu ne mai matukar wahala mu samu inda za mu je a duba mana zuciyarmu kamar haka, kuma abu ne mai matukar tsada da kuma wuya, don haka muna bada cikakken goyan bayanmu akan hakan kuma kasan irin halin kakanakayi da dalibai suke ciki a kasashen Afrika musamman ma mu nan Kamarun"

Neue Herzkatheterlabore an Uni Leipzig
Sashen kula da nazarin zuciyaHoto: picture-alliance/ZB

A dalilin yawan hawan jini dai, a kasar Kamerun kusan mutane dubu 17 ne ke mtuwa a duk shekara saboda awan cutar abu ne mai matukar tsada domin ana kashe kusan Euro 30 wajen bunciken larurar zuciya a kasar ta Kamarun, hakan ne yasa kowace shekara ana samun karuwar masu rasa ransu a kasar. Arthur Zang, shi ne dalibin da ya kirkiro wannan na'ura kuma ya na aiki ne akan wata kwamfutar hannu tsawon shekaru bakoye ya bayyana irin yadda yabi ya kirkiro na'urar dama dalilan kirkiro ta.

"Ni Dalibi ne matashi kuma ina koyan aiki a wani asibiti a Yaounde a kasar Kamarun ta haka ne na gane cewa akwai karancin likitocin zuciya a cikin mutane milliyan 19 na kasar Kamarun ba a samun likitocin zuciya 40 hakan ne yasa nayi sha'awar samar da mafita inda na farko sai na yi wata manhaja na kuma kara inganta ta, ta hakan ne na kirkiri na'urar a shekara ta 2011 wadda na kira Cardiopad"

Bankuna dai a kasar Kamarun sun yi tirjiya wajen tallafa ma Zang ta rancen kudi dan gudanar da aikin sa. Hakan ne ya sa ya yi ta kiraye-kiraye ta kafafen sada zumunta na zamani domin neman tallafi, kuma kiran sa ya samu karbuwa domin kamfanin manhajar kasar Amurka ya bashi Euro dubu 26 wadanda ya yi amfani da su a kamfaninsa ya yi na'urori 20 wadanda ake amfani da su a asibitoci a halin yanzu, kuma wannan na'ura da Zang ya kirkira tana da matukar saukin sarrafa wa, ana sanya wa mara lafiya wata na'ura ta haska bayanai a kirjin mara lafia inda shima can likita zaiga abunda ke damun zuciyar mara lafiya.