Daliban Afirka ta Kudu sun yi yajin karatu | Labarai | DW | 19.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Daliban Afirka ta Kudu sun yi yajin karatu

Daliban jami'o'in Afirka ta Kudu na yajin daukar darasi tare da zanga-zanga domin nuna adawarsu da matakin karin kudin karatu da hukumomin jami'o'in kasar suka dauka.

Studenten der African Leadership Academy

A Afirka ta Kudu, dubban dalibai na wasu jami'o'in kasar guda ukku sun shiga yajin daukar darasi dama gudanar da zanga-zanga domin nuna fushinsu kan tsadar kudin karatun a kasar. Wannan bore na dalibban ya tilasta wa hukumomin jami'o'in ukku da suka hada da jami'ar Rhodes ta garin Grahamstown da ke a Kudu maso Gabashin kasar da jami'ar birnin Cap da ke Kudancin kasar da kuma jami'ar Witwatersrand ta birnin Johannesburg dakatar da aikinsu.

Watanni kusan ukku kenan dai da daliban jami'o'n kasar ta Afirka ta Kudu ke gudanar da zanga-zanga lokaci zuwa lokaci domin tilasta wa hukumomin jami'o'in soke matakin kara farashin kudin karatu da sama da kashi goma daga cikin dari a shekara mai kamawa wanda suka ce ya na hana dalibai bakaken fata wadanda akasarinsu 'ya'yan talakawa ne damar shiga jami'a.