1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar dakatar da cin zarafin Zabiya

Salissou BoukariJuly 7, 2016

Majalisar dokokin Tarayyar Turai ta yi kira ga wasu kasashen nahiyar Afirka, musamman kasar Malawi da su kawo karshen cin zarafin da ake wa Zabiya a kasashensu.

https://p.dw.com/p/1JL9K
Boniface Massah Albino Afrika Malawi
Wani Zabaya mai suna Boniface a kasar MalawiHoto: picture-alliance/dpa/APAM

A iri-irin wadan nan kasashe na Afirka da ke Kudu da Sahara, mutane na hallaka Zabiya tare da yin tsafi da wasu sassan jikinsu, yayin da wasu ma ke tona makarbarta inda aka rufe gawar ta Zabiya domin yin wasu sihirce-sihirce da a cewarsu zai sa su yi arziki nan take. Wannan matsala dai ta yi kamari a kasar ta Malawi, inda daga cikin Zabiyan kasar da aka kiyasta yawansu daga 7000 zuwa 10.000, jami'an tsaron 'yan sanda sun bada rahoton hare-hare da aka kai kan Zabiya 69, tare da kashe 18 daga cikinsu daga shekara ta 2014 kawo yanzu. Tun dai da jimawa kungiyar kare hakin dan Adam ta Amnesty International ta yi Allah wadai da wannan muguwar akida, inda aka kiyasta hare-hare da suka kai 448 kan Zabiya a cikin kasashe 25 na Afirka a shekara ta 2015 kawai.