1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakatar da Najeriya daga wasannin ƙwallon ƙafa na duniya.

October 4, 2010

Hukumar FIFA ta ɗora wa Najeriya haramcin shiga wasannin ƙwallon ƙafa na duniya

https://p.dw.com/p/PVGW
Wasan Argentina da Najeriya yayin gasar cin kofi a Afirka ta KuduHoto: AP

Hukumar wasannin ƙwallon ƙafa ta duniya wato Fifa ta ba da sanarwar dakatar da Najeriya daga wasannin ƙwallon ƙafa na ƙasa da ƙasa. Sanarwar wacce hukumar ta bayyana watanni ukku bayan da Shugaba Good Luck Jonathan ya yanke shawarar dakatar da 'yan wasan Super Eagles daga fagen wasannin, akan rashin taɓuka wani abun kirki a wasannin cin kofin duniya na ƙwallon ƙafa da aka yi a Afirka ta Kudu kafin daga bisani ya dawo kan maganarsa, hukumar ta ce hukumcin yau ya fara aiki. Mahukuntan ƙungiyar dai na zargin gwamnatin Tarayyar Najeriya da yin shisshigi a cikin lamarin wasannin-abin da dokokin hukumar suka haramta. Ya zuwa yanzu dai babu wani ƙarin haske da hukumar ta bayar akan wannan hukunci musamman ma dangane da wa'adin.

Mawalafi: Abdourahamane Hassane

Edita: Halima Balaraba Abbas