Dakatar da masu neman canji daga jam′iyar PDP mai mulki a Najeriya | Siyasa | DW | 23.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dakatar da masu neman canji daga jam'iyar PDP mai mulki a Najeriya

Martani ga matakin da jam'iyyar PDP dake shugabancin tarayyar Nijeriya ta ɗauka na sallamar manyan mambobin ta 19 bisa yiwa jam'iya zagon ƙasa.

default

Saɓani a jam'iyar PDP a Najeriya

A tarayyar Nageriya yanzu haka ana ci-gaba da samun takun saƙa a cikin jam'iyar PDP da ke mulki bayan da jam'iyar ta dakatar da wasu jigajiganta 19 masu neman canji.

Yanzu haka tana can tana ƙasa ta na dabo tsakanin jam'iyar PDP mai mulki da kuma 'ya'yanta 19 masu neman sauyi da ta dakatar.

Yanzu haka dai wannan batu ya ɗauki wani sabon babi dangane da baiyana da shugaban jam'iyar zai yi a ranar Litinin a gaban hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin