1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun soja a Nigeria sun sauka jihar Bayelsa

Gwamnatin tarayya, a Nigeria ta tura jiragen ruwa a kalla 10, dauke da sojoji a Jihar Bayelsa, dake fuskantar riginginmu, tun bayan tserewar gwamnan jihar, Diepreye Alamesia, daga London.

Idan ba a manta ba, ranar litinin da ta wuce ne, a ka bayyana cewar, gwamnan, ya yi shigar mata, domin yaudara jami´an tsaro, da ke tsare da shi ,a kasar Britaniya, dalili da samun sa da aka yi, da wasu magudan kudade.

Bayan dawowar sa, a Yenagoa, babban birnin jihar, Bayelsa, an samu rabuwar kanu, tsakanin masu goya ma sa baya, da masu bukatar a tsige shi, dalili da wannan abin fadi, da ya aikata.