1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Siriya sun zafafa kai hari

Zainab Mohammed Abubakar
January 3, 2017

'Yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Siriya na fuskantar barazana, a yayin da 'yan tawaye suka sanar da kin halartan taron sulhu

https://p.dw.com/p/2VBQt
Syrien syrische Soldaten nach der Zurückeroberung  von Aleppo
Hoto: Getty Images/AFP/G. Ourfalian

Bisa dukkan alamu yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin kasar Siriya na fuskantar barazana, sakamakon zafafa kai hare hare da dakarun gwamnati ke yi kusa da birnin Damaskus. Tuni dai wasu kungiyoyin 'yan tawaye wajen 10 suka ayyana manufarsu na dakatar da shiga tattaunawar sulhu da ake shirin gudanarwa a wannan wata.

Ana shirin komawa teburin sulhu a babban birnin Kazakh watau Astana a karshen wannan wata na Janairu, sai dai 'yan tawayen sun ce za su janye ne saboda abun da suka kira "watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki hudu da Damaskus ta yi".

Rasha ce dai ta ke shirya gudanar da zaman sulhun tare da tallafin gwamnatin Siriya, a daya hannun kuma da Turkiyya da Iran da ke goyon bayan 'yan tawayen kasar.